Babaji

5698 Posts

SDP ta kori El-Rufa’i na tsawon shekaru 30

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa, SDP ta kori tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa'i daga jam'iyyar na tsawon shekaru 30 bayan samunsa da laifin saɓa wa dokokinta da na zaɓe. Bayanin hakan na ƙunshe a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, wadda ya fitar ranar Litinin, inda ya ce SDP ta ɗauki matakin ne a ƙarƙashin dokoki da tsare-tsaren jam'iyyar da kuma sashin dokar zaɓe na ƙasa da ya ba ta damar zaɓar wanda ta ke so ya zama mambanta. Jam'iyyar ta kuma gargaɗi mambobinta a…
Read More

2027: Majalisar Wakilai na yin ƙudirin haɗe zaɓukan shugaban ƙasa da gwamnoni rana ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Wakilai ta fara yunƙurin sauya tsarin gudanar da zaɓuka a Nijeriya, yayin da ta ke neman a mayar da yin duka zaɓuka guda biyar da suka haɗa da na shugaban ƙasa, gwamnoni, ƴan majalisar dokoki na tarayya da ƴan majalisun jihohi a rana ɗaya. Hakan wani yunƙuri ne na yin kwaskwarima ga sabuwar dokar zaɓe ta 2025 da nufin samar da gyare-gyare ga harkokin gudanar da zaɓe a Nijeriya. Ƙudirin kafa dokar zaɓe a rana guda zai taimaka wajen rage adadin kuɗaɗen da ake kashewa a yayin gudanar da harkokin zaɓuka a faɗin…
Read More

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar lauyoyi shida sun nemi a biya N20m ga kowannensu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban Makarantar Lauyoyi guda shida sun nemi a biya Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa ga kowane ɗaya daga cikin ɗaliban. A ranar Asabar aka yi garkuwa da ɗaliban, waɗanda suak taho daga garin Onitsa dake jihar Anambara domin zuwa reshen makarantar dake Yola a Jihar Adamawa. Lamarin ya ayyukan a yankin Wukari dake Jihar Taraba, a titin iyakar Ƙaramar Hukumar da yankin jihar Benuwai. Ɗaya daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su a wata hira da wani takwaransa, ya ce ana buƙatar N20m a matsayin…
Read More

Iyalan Buhari sun koma Kaduna kwanaki 12 da jana’izarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyalan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wato A'isha Buhari da tsohuwar matarsa tare da ƴaƴansu, sun yi ƙaura daga Daura zuwa Jihar Kaduna, kwanaki 12 da yin jana'izar tsohon shugaban. Manyan jami'an gwamnati ne suka marabce su domin girmamawa ga marigayin. An ruwaito cewa, tsohuwar matar shugaban - Aisha Buhari, ta taho ne tare da ɗanta Yusuf Buhari, ƴarta Zahra Buhari da kuma suaran mambobin iyalan inda suka sauka a sansanin sojojin sama dake Kaduna, ranar Lahadi. Komawarsu ta nuna kawo ƙarshen jimamin rashin marigayi Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga…
Read More

An buƙaci al’ummar Dawakin Tofa su bada haɗin kai ga riga-kafin zazzaɓin cizon sauro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Alhaji Anas Mukhtar Bello Ɗan-Maliki, ya yi kira ga al'umma a ƙaramar hukumar da su bada haɗin-kai wajen gudanar da shirin bayar da maganin riga-kafin zazzaɓin cizon sauro ga yara ƙanana. Ɗan-Maliki, wanda Shugabar Sashen Kula da Lafiya a Matakin Farko, Hajiya Balaraba B. Gambo, ta wakilta, ya ƙarfafa gwiwar mazauna ƙaramar hukumar da su halarci taron raba gidan sauro da zarar an ƙaddamar da shirin a cibiyoyin da aka ware. A sanarwar da jami'ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Ciyaman ɗin ya kuma…
Read More

Neja: Mutane da dama sun rasu bayan kifewar kwale-kwale a Shiroro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fasinjoji da dama sun rasu a yayin da wata kwale-kwale ta kife a Kogin Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Lamarin ya auku ne a ranar Asabar, kamar yadda Hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar, NSEMA ta bayyana. A sanarwar ta fitar ranar Lahadi ta hannun Daraktan yaɗa labaranta da ayyuka na musamman, Ibrahim Hussaini, NSEMA ta ce kwale-kwalen ya nutse ne a tsakiyar kogin bayan ɗebo fasinjojin da ba a ƙayyade adadinsu ba da kayayyaki waɗanda suka taho daga kasuwar Zumba. Daraktan ya ce, an yi nasarar ceto matuƙin kwale-kwalen tare da wasu…
Read More

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban makarantar lauyoyi a hanyarsu ta zuwa reshenta na Yola

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An shiga halin zaman ɗar-ɗar acikin ɗaliban Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya bayan zargin ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗalibai guda shida na makarantar akan hanyar Benuwai zuwa Taraba. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a daren ranar Asabar wayewar Lahadi, wanda ya rutsa da ɗaliban waɗanda suka taho daga Onitsa a jihar Anambara domin koma wa karatunsu a reshen makarantar dake Yola, Jihar Adamawa. Ɗaya daga cikinsu mai suna Damilare Adenola ta tabbatar wa jaridar NewsPoint Nigeria faruwar al'amarin inda ta ce abokan karatunta guda shida aka yi garkuwa da…
Read More

Shettima zai halarci taron tsare-tsaren abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya a Habasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai halarci taron tsare-tsaren abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya karo na biyu, wanda za a yi a Addis Ababa, Babban Birnin ƙasar Habasha. Za gudanar da taron ne daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Yulin nan kamar yadda Kakakinsa Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda, ranar Lahadi. An shirya babban taron ne da haɗin-gwiwar gwamnatocin Habasha, Italiya da Majalisar Ɗinkin Duniya inda za a tara shugabannin ƙasashen duniya. Za a yi nazari game da nasarorin da aka cimma a zangon farko da ƙaddamar da tsare-tsaren inganta harkokin…
Read More

Akpabio da Opeyemi sun kusa ba hammata iska a zazzafan zaman shugabannin Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu saɓani a yayin wani zama da aka gudanar tsakanin shugabannin Majalisar Dattawa game da lokacin tafiya hutun wata biyu na majalisa da aka saba yi kowace shekara. A yayin zaman ne muryoyi suka shaida wa SaharaReporters cewa an samu saɓanin ne a tsakanin shugabannin a lokacin da ake ƙoƙarin cimma matsaya kan batun shirin ɗage tafiya hutun. Lamarin, wanda ya auku a ranar Laraba a yayin wata ganawar sirri, ya sa an yi musayar kalamai cikin fushi tsakanin Shugaban majalisar Godswill Akpabio da kuma jagora a majalisar, Opeyemi Bamidele, inda suka kusa…
Read More

Kogi: Tashar Radio Nigeria ta ɗauke bayan ƴan fashi sun farmake ta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tashar Rediyo Nijeriya mai aiki a zangon FM 101.5 a Jihar Kogi ta samu tsaiko bayan da wasu ƴan fashi suka kai wa tuƙullumar watsa labaranta mai tsadar miliyoyin kuɗaɗe hari, inda suka sace wasu daga kayayyakin ofishinta. Janar Manaja ta tashar, Momoh Jimoh Adeiza a wani saƙo da aka fitat, ta ce lamarin ya auku ne a safiyar ranar Asabar. An ruwaito cewa, ɓarayin sun shafe tsawon sa'o'i uku suna fashi a gidan rediyon. Adeiza ta shaida wa manema labarai cewa sun tashi da safe kwatsam suka tarar da an lalata ofishin nasu…
Read More