27
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar Shugaba Bola Tinubu ya taya Super Falcons ta Nijeriya murnar lashe Kofin Ƙasashen Afirka (WAFCON) karo na 10. Super Falcons sun yi nasarar ne bayan farfaɗowa da suka yi a yayin da aka tafi hutun rabin lokaci ana shan su ƙwallo biyu da nema, inda daga bisani suka yi nasara da ci 3 da 2 akan takwarorinsu na Moroko. A saƙon da aka wallafa a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya bayyana farin cikinsa ga ƙungiyar, inda ya ce sun yi amfani da damar da suka samu wajen kare martabar Nijeriya.…
