
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya umarci a yi cikakken bincike game da zargin Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Namadi da hannun acikin belin wani dillalin ƙwaya mai suna Sulaiman Aminu Ɗanwawu.
Hakan ya biyo bayan cecekuce da al’umma ke yi akan rahoton da ke nuna kwamishinan yana da hannu a lamarin musamman yadda aka ga sunansa takardun da aka gabatar wajen bada belin dillalin ƙwayar.
Hakan na ƙunshe a cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa inda ya ce, Gwamna Abba a ƙoƙarinsa na magance matsalar ya naɗa kwamitin na musamman ƙarƙashin jagorancin Barista Aminu Hussain, wato mai ba shi shawara kan harkokin shari’a domin ya gudanar binciken akan al’amarin.
Ya bayyana cewa, an ɗora wa kwamitin nauyin samar da cikakken bayani game da batun tare da bada shawarwarin da suka dace.
Mambobin kwamitin sun haɗa da:
- Barr. Aminu Hussain, Shugaba
- Barr. Hamza Haladu, Mamba
- Barr. Hamza Nuhu Dantani, Mamba
- Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar, Mamba
- Maj. Gen. Sani Muhammad (Rtd.), Mamba
- Comrade Kabiru Said Dakata, Mamba
- Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya.
A yakin sanar da naɗin kwamitin, gwamnan ya koka game zargin, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tuƙuru wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar.
