Babaji

5698 Posts

Kano: Kwamishina ya yi wa dillalin ƙwaya lamuni a kotu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a jihar Kano sun sanya alamar tambaya akan Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Namadi bayan da ya yi lamuni ga wani shahararren dillalin miyagun ƙwayoyi mai suna Suleiman Ɗanwawu a kotu. Ana tuhumar Ɗanwawu ne da laifuka takwas masu alaƙa da safarar ƙwayoyi, wanda Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shigar akansa. A ranar 16 ga watan Yuli ne aka bada belin sa a ƙarƙashin hukuncin Mai Shari'a M.S Shu'aibu na Babbar Kotun Kano. A yayin haka ne Alƙalin ya sanya sharuɗɗa masu tsauri waɗanda daga ciki akwai ya nemo…
Read More

Bayan G-Fresh, kotu ta tasa ƙeyar mawaƙi Hamisu Braker gidan yari bisa wulaƙanta Naira

Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kano ta ɗaure shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da Al-Amin G-Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na Naira. Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda ta tuhumi Hamisu Sa'id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G-Fresh) da yin liƙin kuɗi yayin wasu bukukuwa. Cikin rahoton da EFCC ta fitar, kotun ta kama G-Fresh da laifin "liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi na N1,000 da suka kai N14,000" a shagon Rahama Saidu a watan Nuwamban 2024. Kazalika, kotun ta kama Breaker da…
Read More

‘Lokacin daina yaƙi a Gaza ya yi’: Faransa na shirin ayyana Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Faransa ta sanar da shirin ayyana ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci a watan Satumba yayin babban zaman Majalisar Ɗinkin Duniya. Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya sanar da hukuncin a daren ranar Alhamis wayewar Juma'a, inda ya ce hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a shiyyar Gabas ta Tsakiya, kamar yadda ya bayyana a wani saƙo ta kafar X. Ya ce, babban abinda ke gabansu a yanzu shi ne kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da ceto al'ummar yankin. Ya bayyana cewa, wajibi ne su gina ƙasar tare da tabbatar da…
Read More

Sai yaro ya kai shekaru 12 zai shiga sakandare a sabon tsarin ilimi – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ma'aikatar Ilimi ƙarƙashin jagorancin Minista, Tunji Alausa ta sanar da sabuwar doka dake nuna cewa sai ɗalibi ya kai shekaru 12 sannan za a ba shi damar fara karatu a makarantar sakandare bayan karatun firamare. Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sabon tsarin ne a wani saƙon tsare-tsare ga makarantun kuɗi, wanda ma'aikatar ta fitar a kwanan nan da nufin inganta tsarin ilimin yara a makarantun. A cewar saƙon, an tsara ilimin matakin farko a Nijeriya cikin shekaru tara inda za a yi shida a firamare, sai kuma uku a ƙaramar sakandare. A…
Read More

Gwamnatin Tinubu ba ta mayar da Arewa saniyar ware ba – Fadar Shugaban Ƙasa ga Kwankwaso

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata zargin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya yi kan cewa shugaba Tinubu na karkatar da ayyukan raya ƙasa ga yankin Kudu a yayin da aka yi watsi da yankin Arewa. PREMIUM TIMES ta rawaito muku yadda kwana ɗaya bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa a Abuja, Kwankwaso ya zargi shugaban da mai hankali wajen bunƙasa yankin Kudancin ƙasar. Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP a shekarar 2023 ya yi wancan zargin ne a lokacin taron nazarin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya wanda gwamnatin Kano ta shirya. “Bari na bai wa gwamnatin…
Read More

Ku ƙara himma wajen hidimta wa al’umma saboda har yanzu suna fama – Tinubu ga gwamnoni

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam'iyyar APC da su warware matsalolin ci-gaba da al'umma suke fuskanta a jihohinsu. A lokacin da ya ke magana taron kwamitin zartarwar jam'iyyar (NEC)a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ce har yanzu ƴan Nijeriya suna fama da tsananin rayuwa da cigaban da nuna rashin gamsuwa da salon tafiyar mulkinsu. Ya ce, akwai buƙatar gwamnonin su mayar da hankali wajen inganta rayukan al'umma tun daga matakin ƙauyuka ta yadda za a samu sauƙi halin matsalolin da suke fuskanta. Ya jaddada cewa ƙofa…
Read More

An zartar wa shahararren jarumin fim hukuncin kisa a Chana kan halaka budurwarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An zartar wa shahararren jamrumin fina-finan Chana kuma mawaƙi, Zhang Yiyang hukuncin kisa bayan samun sa da laifin kashe budurwarsa mai ƙananan shekaru, lamarin da ya sa ya zama jamrumi na farko a Chana da aka taɓa yi irin haukuncin. Wata kotun al'umma dake yankin Xianyang a Arewacin Shaanxi ta bayyana hakan a wani rahoton da ta fitar a watan Yuli, 2025. Ta ce, an yi wa jarumin mai shekaru 32 hukuncin ne a ranar 18 ga watan Disambar 2024 bayan tabbatar da ya aikata laifin. A shekarar 2022 ne Zhang ya daba wa…
Read More

PDP ta ayyana ranar babban taronta na ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar PDP ta kammala zaman kwamitin zartarwata (NEC) inda ta ayyana ranakun gudanar da babban taronta a watan Nuwamba, 2025. A yayin zaman, wanda aka yi a Abuja ranar Alhamis, aka ayyana ranakun 15 da 16 ga Nuwamba a matsayin lokacin babban taron wanda za yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo. Kwamitin Zartarwar jam'iyyar ya tabbatar wa mambobi da ɗaukacin ƴan Nijeriya cewa PDP tana nan da ƙarfinta kuma kan ƴaƴanta a haɗe ya ke wajen ganin ta cimma nasarorin da ta saka a gaba. Ya umarci Shugaban jam'iyyar, Ilya Damagum da Sakatarenta,…
Read More

Zan ɗauki matakan shigo da ƙarin gwamnonin PDP cikin APC, inji sabon shugaban jam’iyya Farfesa Yiltwatda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sabon shugaban jam'iyyar APC na Ƙasa, Nentawe Yiltwatda ya ci alwashin ɗaukar matakai masu tsauri a matsayinsa na shugaban jam'iyyar. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin hira da gidan talabijin na Channels sa'o'i kaɗan bayan naɗa shi a muƙamin a ranar Alhamis. Ya ce, zai tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki na jam'iyyar akan shawarar da suak dace wajen tafiyar da jam'iyyar cikin tsari tare da kai ta ga nasara. Ya kuma ce, zai yi koyi da Shugaba Bola Tinubu wajen tafiyar da mulkin ƙasa ta hanyar amfani da matakai masu tsauri, waɗanda a cewarsa hakan…
Read More

Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abinda ya kira watsi da yankin Arewa, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin Nijeriya ta amfani da albarkatun ƙasar. Ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki na 2025 da aka gudanar a Kano, ranar Alhamis. "Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan." Kwankwaso ya kuma zargi jam'iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori…
Read More