Babaji

5698 Posts

Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Makonni kaɗan da rasuwar sarkin masarautar Ijebu, Oba Sikiru Adetona, wani babban sarkin gargajiya kuma sark8n Gusau a Jihar Zamfara, Dakta Ibrahim Bello ya rasu. Sarkin, wanda ya gaji mahaifinsa da ya rasu shekarar 2015, ya rasu ne a Abuja bayan shafe shekaru 71 a duniya. Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya tabbatar da hakan a wata takarda, ranar Juma'a. Gwama, Dauda Lawal na jihar ya yi jimamin rashin sarkin tare da jajenta wa iyalai da ɗaukacin al'ummar jihar bisa rashin. Sarkin ya kasance ma'aikacin gwamnati da ya kai matsayin babban sakatare a…
Read More

An tasa ƙeyar shahararren ɗan TikTok, Al-Amin G-Fresh zuwa gidan yari kan wulaƙanta Naira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Kano ta yanke wa sanannen ɗan TikTok a jihar, wato AL-Amin G-Fresh hukuncin wata biyar a gidan yari bayan samun sa da laifin wulaƙanta takardun Naira. Mai Shari'a Sale Musa Shuaibu ya gabatar da hukuncin bayan da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta maka shi a kotun. Bayan karanta masa abin da ake tuhumar sa a kai, G-fresh ya amsa laifinsa. Daga nan ne kotun ta yanke masa hukuncin tare da zaɓin biyan tarar Naira 200,000. An samu mai laifin ne da watsa bandir-dandir ɗin ƴan…
Read More

Tsohon ɗan wasan kokawa, Hulk Hogan ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kamfanin shirya wasan dambe na WWE ya tabbatar da rasuwar fitaccen ɗan wasan kokawa Hulk Hogan. Hogan, wanda asalin sunansa Terry Bollea, na ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan kokawa a shekarun 1980 da 1990, kuma ya shahara a wasu fannonin nishaɗantarwa daban-daban. Hogan, wanda ya shafe shekaru 71 a duniya, ya rasu ne bayan samun ɗaukewar bugun zuciya a gidansa dake birnin Clearwater. Ganin haka ya sa aka garzaya da shi wani asibiti a safiyar ranar Alhamis, inda aka tabbatar da mutuwarsa. Hakan ya faru ne makonnin kandan da matar Terry Bollea ta…
Read More

An yanke wa tsohon soja hukuncin rataya kan laifin fashi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa-Ibom ta yanke wa wasu ƴan fashi guda biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin fashi ga wasu ƴan adaidaita sahu a babban birnin jihar, Uyo. Ɗaya daga cikin su shi ne Lance Corporal Promise Okokon Usoro, wanda tsohon soja ne da aka sallame shi a aiki daga bataliya ta 6 ta rundunar sojojin Nijeriya dake Barikin Ibagwa a Ƙaramar Hukumar Abak. Usoro mai shekaru 41, an same shi ne da bindiga ƙirar AK-47 da laifin yin fashi ga wani mai suna Peter Daniel Okon…
Read More

Jami’an NIS sun nemi hana Sanata Natasha fita waje bayan ƙwace mata fasfo a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar ranar Alhamis ne a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja wani al'amari da ke kama da wasan kwaikwayo ya faru a yayin da jami'an Hukumar Shige da Fice (NIS) suka dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga karɓar tikitin jirgin zuwa Landon tare da ƙwace mata fasfo. Lamarin da ya jefa matafiya a filin cikin al'ajabi da ƙoƙarin samar da tsaiko ga harkokin al'umma. Wani shaida ya ce, Natasha ta je filin jiragen ne tare da mijinta, Cif Emmanuel Uduaghan domin fita ta jirgin British Airways. Saidai, kafin su karɓi tikitin…
Read More

Ministan Jinƙai, Yiltwatda ya zama sabon shugaban APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC ta shirya sanar da Ministan Jinƙai, Farfesa Nentawe Goshwe Yiltwatda a matsayin sabon shugabanta biyo amincewa da shi da gwamnoni da shugabannin jam'iyyar a mataki na jihohi suka yi. Hakan na zuwa ne bayan gudanar da zama da yin shawarwari da masu-ruwa-da-tsaki a safiyar ranar Alhamis. A gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar. Baki ɗaya gwamnonin sun halarci taron face, na Legas da Akwa-Ibom, waɗanda suka samu wakilcin mataimakansu. Tun a ranar Laraba ne gwamnonin suka je Fadar Shugaban Ƙasa…
Read More

Rashin tsaro: Gwamnatin Yobe ta sake buɗe kasuwannin Buni-Yadi da Kukareta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Yobe tare da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro sun yi nasarar sake buɗe kasuwannin Kukareta da Buni-Yadi, waɗanda aka rufe su a baya sakamakon matsalolin rashin tsaro da yankunan suke fuskanta. An rufe kasuwannin, waɗanda ke Ƙananan Hukumomin Gujba da Damaturu ne domin rage damar samar da abinci ga mayaƙan ƴan ta'adda da ke addabar al'umma a ƴan kwanakin nan. Mai bai wa gwamnan jihar, Mai Mala Buni Shawara kan Harkar Tsaro, Dahiru Abdulsalam ya shaida wa manema labarai hakan jim-kaɗan bayan kammala zama akan lamuran tsaro a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan, Barde Gubana…
Read More

EFCC ta kama ɗaliban BUK 25 bisa zargin damfara a yanar gizo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta kama mutane 25 bisa zargin su da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo a Kano. Kakakin hukumar, Dele Oyewale a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya ce an kama mutanen ne a yankin unguwar da ke daura da sabon sashin Jami'ar Bayero (BUK), wato New Campus. Ya ce, "baki ɗaya waɗanda ake zargin ɗalibai ne da ke karatun digiri a BUK." Ya kuma ce, daga cikin ababen da aka ƙwato a hannun ɗaliban akwai wayoyin hannu, kwamfotocin 'laptop', na'urorin…
Read More