24
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL a karo na biyu cikin sati guda ya rage farashin fetur. Jaridar 'Daily Post' ta ruwaito cewa a ranar Laraba aka ga gidajen man kamfanin sun rage farashin kowace lita daga N895 zuwa N890. Hakan ya nuna an samu ragin N5 idan aka kwatanta da N895 da ake sayerwa a baya. Tuni gidajen man a yankunan Kubwa, Gwarimpa, Wuse, da wasu wurare a Abuja suka rage farashinsu a famfuna zuwa sabon farashin. Yayin da NNPCL ya yi ragin farashin, gidajen man da ke dako daga Matatar Ɗangote…
