Gwamna Uba Sani ya raba gidaje ga mutanen da iftila’in ƴan bindiga ya shafa a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ƙaddamar da sababbin gidaje ga mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa, a ƙarƙashin ayyukan gidauniyar Ƙatar Sanabil na ƙasar Ƙatar da gwamnatin jihar.

Ayyukan da gidauniyar suka yi sun ƙunshi samar da gidaje da asibitoci da babban shagon sayeyya domin farfaɗo da walwalar al’ummar da ayyukan ƴan ta’addan ya shafa na tsawon lokaci a jihar.

Da ya ke magana yayin taron raba gidajen, Gwamna Uba Sani ya ce shirin na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatinsa ta ke ɗauka wajen inganta rayukan al’umma musamman waɗanda iftila’i ya afka musu.

Ya ce, hakan wani yunƙuri ne na ƙarfafa musu musamman wajen sake dawo da martaba da sabunta fata a gare su.

Gwamnan ya bayyana cewa, ayyukan ƴan bindiga a jihar sun yi sanadin lalata ƙauyuka da dama da ɗaiɗaita makarantu da wargaza sauran al’amuran al’umma na yau da kullum, yana mai cewa duk da ƙoƙarin dakarun tsaro wajen dawo da zamani lafiya, haka kuma wajibi ne su inganta rayukan jama’ar da suka tsinci kawunansu a irin halin.

Sannan, a ƙarƙashin shirin gidauniyar Ƙatar Sanabil, an raba wa iyalan da lamarin ya shafa babura masu taya uku, injinan markaɗe, kayan gyaran gashi da kuma kayayyakin gyare-gyare domin dawo da tattalin arziƙinsu.

Bugu da ƙari, gwamnan ya ƙaddamar da sabuwar makaranta domin samun karatu a kyauta ga ƴaƴansu da asibiti gami da cibiyar koyar da sana’o’i ga matasa da mata.

By Babaji