Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gamayyar ƙungiyoyin Ƙwadago na NLC da TUC a Jihar Katsina sun bayyana rashin goyon bayan su ga shirin gwamnatin jihar na sauya fasalin dokar fansho da majalisar dokoki ta Jihar Katsina ke shirin aiwatarwa.
A wani taron manema labarai wanda ƙungiyar ta kira, shugaban ƙungiyar manyan ma’aikata TUC na Jihar Katsina, Muntari Abdu Ruma, a madadin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon ya bayyana rashin amincewar su da yunƙurin majalisar.
“Yunƙurin sauya dokar ya saɓawa dokar fansho da muka sani kuma muka yarda ake aiwatar da ita a yanzu.
“Ba ma goyon shirin majalisar jiha na sauya dokar daga wadda ake amfani da ita a halin yanzu, sanin kowane an fara cirewa ma’aikata kuɗi daga watan Disamban bara na 2024”, Gamayyar ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana.
Muntari Ruma ya ƙara da cewa “dalilin da yasa ba zamu amince ba shine, dokar da majalisar ta ke shirin yi a jihar Katsina itace ta tsarin fenshon da ake amfani da ita a matakin gwamnatin tarayya wadda ta jefa yan fensho na gwamnatin tarayya cikin wahalhalu.
Taron ya samu halartar Shugaban ƙungiyar Kwadago ta jihar Katsina, (NLC)Comrade Hussaini Hamisu Yanduna da S
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi na Jihar Katsina. NULGE, Comr. Nasiru Wada Maiadua. da sauran Shugabanni da mambobin ƙungiyoyin ƙwadago a faɗin jihar.
