21
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin ne wata tawagar ƴan sandan da suka yi ritaya a Abuja ta karaɗe tituna inda ta yi zanga-zangar lumana game da halin rashin kula yadda ya dace da suke fuskanta da waɗanda ke aiki har yanzu a rundunar daga gwamnati. An gudanar da zanga-zangar ne a ƙarƙashin jagorancin mai fafutukar ƴancin al'umma, Omoyele Sowore, wanda ya shiga sahun masu zanga-zangar da nufin janyo hankalin Gwamnatin Tarayya. Sun koka game da rashin gamsuwa da yadda ake kula da su tsawon shekaru akan rashin biyan su kuɗaɗe fansho da kuma yin watsi da…
