Bayan watanni, jirgin N150bn na Fadar Shugaban Ƙasa ya dawo Abuja daga Afirka ta Kudu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sabon jirgin Fadar Shugaban Ƙasa da aka sayo a Naira biliyan 150 ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida Nijeriya tun tsawon watanni da aka kai shi ƙasar Afrika ta Kudu don sauya masa launi zuwa kalan tutar Nijeriya, wato launin kore da fari.

An sayo jirgin, ƙirar Airbus A330-200 a watan Agustan 2024, wanda aka gan sa a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja a ranar Laraba.

Tun a watan Fabarairun 2025 jirgin ya ke ajiye inda daga bisani aka fita da shi zuwa ƙasar da nufin yi masa fenti da wasu ƴan gyare-gyare.

Wani jami’i daga fadar da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar da isowar jirgin ga jarida PUNCH, inda kuma ya ce nan ba da jimawa jirgin zai fara aiki a fadar, saidai babu masaniya akan ko shugaban ƙasar zai yi amfani da jirgin a tafiyarsa ta gaba.

A kwanan nan ne Shugaba Tinubu zai je Jihar Ogun domin jajenta rasuwar marigayi Sarkin Masarautar Ijebu, Oba Sikiru Adetona, wanda ya rasu a ranar 13 ga watan Yuli bayani shafe shekaru 91 a duniya.

An sayi jirgin ne, wanda ke ɗauke da ɗakin bacci, makewayi, ɗakin taro, da kayan sadarwa, da nufin maye gurbin tsohon jirgin Fadar, wanda marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke amfani da shi a lokacin da ya ke kan mulki duba da tsufarsa.

By Babaji