Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta zama Sakatariyar ƙungiyar ‘First Ladies Against Cancer (FLAC)’ ta ƙasa, gamayyar matan gwamnonin Najeriya masu fafutukar yaƙi da cutar kansa ta hanyar bayar da shawarwari, gyara manufofi da kuma shiga tsakani kai tsaye ga al’umma.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Gusau ranar Asabar, mai ɗauke da sa hannun sakatariyar yaɗa labaranta, Rabi’atu Yusuf.
Sanarwar ta bayyana cewa, naɗin nata ya nuna matuƙar karramawa da irin gudunmawar da ta bayar wajen haɓaka kiwon lafiya, musamman a fannin wayar da kan jama’a game da cutar daji, rigakafin cutar daji da kuma kula da masu fama da cutar a jihar Zamfara.
A sabon aikinta, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewar, za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da takwarorin ta matan gwamnoni don ƙara ƙaimi da kuma samar da kayan aiki don inganta tsarin kula da cutar daji musamman ga al’ummomin da ba su da ƙarfi.
“Naɗin nata ya biyo bayan bikin bayar da tallafin cutar daji na FLAC kwanan nan da aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar Imo Asokoro, Abuja, inda suka tattauna kan ƙarfafa ayyukan ceto da kuma inganta yaƙi da cutar daji a Nijeriya ”.
“Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bambanta kanta ta hanyar ayyuka masu tasiri waɗanda ke amfanar da masu rauni kai tsaye ƙarkashin jagorancinta”.
Sanarwar ta ce, Jihar Zamfara ta sha yin gwajin cutar kansar mama kyauta, da wayar da kan jama’a, da kuma ɗaukar nauyin yi wa masu fama da cutar kansa fiye da 100 tiyata.
“Taimakon da ta bayar na ₦ 3.5 miliyan don kula da marasa lafiya masu fama da cutar kansa ya nuna tausayi da kuma fahimtar ƙalubalen kiwon lafiyar jama’a.”
A matsayin Sakatariyar FLAC, ana sa ran Hajiya Huriyya za ta ƙara wani sabon salo ga ƙungiyar gamayya ta ƙasa, gami da bayar da shawarwari game da manufofin kiwon lafiya da suka haɗa da, taimakon al’umma, da kula da marasa ƙarfi.
“Naɗin nata ya kuma nuna cewa Arewacin Najeriya na da hannu wajen tattaunawa kan manufofin da suka shafi cutar kansa da kuma bayar da hidima”.
Blueprint Manhaja ta tattaro cewa bikin bayar da gudummawar da aka yi a Abuja ya nuna bayar da tallafin kuɗi ga manyan ƙungiyoyi biyu masu tallafawa cutar kansa da suka haɗa da Network of People Impacted by Cancer in Nigeria (NePICiN) da Health & Psychological Trust Center, wanda ya ƙara nuna aniyar FLAC na inganta rayuwar masu fama da cutar kansa.
Shugabar FLAC kuma Uwargidan Gwamnan Jihar Imo, Barista Chioma Hope Uzodimma, ta yaba da shirin a matsayin “babban jari a rayuwa, mutunci, da daidaiton lafiya.”
Sanarwar tayi nuni da cewar taron ya samu halartar fitattun matan gwamnoni da suka haɗa da H.E. Lami Ahmadu Fintiri (Mataimakin Shugaban FLAC), H.E. Dr. Linda Ayade, H.E. Monica Ugwuanyi, H.E. Hajiya Zainab Nasir Idris, H.E. Agyin Kefas, da sabuwar Sakatariyar FLAC, H.E. Hajiya Huriyya Dauda Lawal”.
Hakazalika, ɗaukakar da mai girma gwamna ta samu kan wannan rawar ta ƙasa ba wai kawai ya ƙara fito da martabarta a fannin kiwon lafiya ba, har ma yana ƙara ƙarfafa gwiwar guiwar Zamfarawa wajen kawo sauyi kan harkokin kiwon lafiyar al’umma da mata ke jagoranta”. Sanarwar ta ƙara da cewa.
