
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na jihar Katsina ya samu hatsari a hanyar Daura zuwa Katsina a Lahadi, sai dai bai samu wani rauni mai tsanani ba.
Kamar yadda Babban Sakataren yaɗa labaransa, Muhammadu Kaula ya sanar, motar Gwamna Raɗɗa ta yi taho mu gama ne da wata motar haya ƙirar Golf da ya kwaso fasinjoji fiye da kima, lamarin da ya yi sanadin injin motar ta fita.
Kaula ya bayyana cewa, gwamnan na cikin ƙoshin lafiya, sannan yana miƙa godiyarsa ga jama’ar da suke ta aika masa da saƙon jaje.
Gwamnan dai yayi ta kai-komo a hanyar Katsina zuwa Daura domin karɓar gaisuwar rasuwar marigayi tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Babu dai wani ƙarin bayani game da waɗanda suka samu raunuka a hatsarin, saidai wata majiya ta bayyana cewa fasinjojin da ke cikin motar hayar sun karairaye.
