Bayan kusan shekaru 20 a doguwar suma, Yariman Saudiyya ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masarautar Saudiyya ta sanar da rasuwar Yarima, Alwaleed bin Khalid bin Talal, wanda ake kira da ‘Yarima mai bacci’.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne Yariman ya rasu bayan shafe shekaru 35 a duniya, waɗanda daga ciki, ya yi 20 acikin doguwar suma.

Mahaifin yariman, Khalid bin Walid ya faɗi hakan a shafinsa na X, inda ya yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa da rahama.

“Kasancewar zuciyoyinmu sun yi imani da duk abin da Allah ya hukunta, amma a cikin alhini, muna jimamin ɗanmu, abin ƙaunarmu Yarima Alwaleed bin Khalid bin Talal bin Abdulaziz Al Saud, Allah jiƙan sa, ya koma ga Allah maɗaukaki a yau”, kamar yadda bayanin ya nuna.

A shekarar 1990 aka haifi yariman, inda ya samu wani mummunan hatsarin mota a shekarar 2005 lokacin da ya ke karatu a kwalejin horar da sojoji.

By Babaji