Kperogi ya bai wa Aisha Buhari haƙuri kan ikirarin ƙarewar aurenta da Buhari gabannin rasuwarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai sharhi akan harkokin al’umma kuma mazaunin Amurka, Farfesa Farooq Kperogi ya miƙa buɗaɗɗen saƙon bada haƙuri ga tsohuwar matar shugaban ƙasa, Aisha Buhari bisa ikirarin da ya yi cewa aurenta ta da marigayi Muhammadu Buhari ya ƙare.

A ranar Laraba ne Farfesan, wanda asalinsa ɗan Nijeriya ne ya yaɗa batun, wanda ke nuna cewa auren Aisha da Buhari ya ƙare tun gabannin rasuwarsa.

A cewarsa, Aisha ta canza sunan Buhari da na mahaifinta, wato ta koma amfani da ‘Aisha Halilu’ a madadin Aisha Buhari.

Ya kuma ce, da fari ta ƙi amince wa zuwa Landon inda ya ke jinya domin ba shi kula, wanda sai daga baya sannan ta je.

Saidai, a wani saƙo da ya sake wallafawa a ranar Lahadi, Kperogi ya yarda cewa ya tafka babban kuskure wajen zargin rabuwar auren nasu jim-kaɗan bayan kammala wa’adin mulkin Buhari a 2023.

Ya ce, ya yi da-na-sanin yaɗa batun wanda ya ce cutarwa ne ga mutunci da kimar tsohuwar matar shugaban ƙasar, yana mai neman afuwa a gare ta na ta yafe masa.

Farfesan ya bayyana cewa, yaɗa irin waɗanda labaran ga al’umma kuskure ne daga ɓangarensa komai sahihancinsa, yana mai cewa ba kowane irin labari ba ne za a yaɗa wa al’umma.

Hakan ya biyo bayan da wani mataimaki ga Aisha, Alhaji Sani Zorro ya tattauna da Farfesan, inda ya tabbatar masa da cewa auren nasu yana na daram.

By Babaji