

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohuwar matar shugaban ƙasar, Hajiya Aisha, ta musanta rahoton rabuwarta da marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari gabannin rasuwarsa.
Farfesa Farooq Kperogi, wanda shi ya fitar da labarin da ba haka ya ke ba a yanar gizo, ya fito ya ba ta haƙuri bisa al’amarin a ranar Lahadi.
Hakan ya biyo bayan da wani mataimaki ga Aisha kan harkokin al’umma, Alhaji Sani Zorro, wanda shi ma ɗan jarida ne kamar sa ya tattauna da Farfesan, inda ya tabbatar masa da cewa auren nasu yana na daram.
Kperogi a saƙon da ya sake wallafawa ya ce, ya yi da-na-sanin yaɗa batun wanda ya ce cutarwa ne ga mutunci da kimar tsohuwar matar shugaban ƙasar, yana mai neman afuwa a gare ta na ta yafe masa.
Farfesan ya bayyana cewa, yaɗa irin waɗanda labaran ga al’umma kuskure ne daga ɓangarensa komai sahihancinsa, yana mai cewa ba kowane irin labari ba ne za a yaɗa wa al’umma.
Ya kuma tabbatar da cewa, bai yi hakan ba da nufin cutar da ita ba, saidai kuskure ne da aka samu daga gare shi, yana mai jaddada ba ta haƙuri akan kalaman nasa akanta.
