
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce za ta koma zuwa zaman majalisa a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025 bisa hukuncin kotu, duk da cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ƙalubalanci hakan a yayin da ya ɗaukaka ƙara a kotu.
A wata hira da ita yayin wani shiri a mazaɓarta ranar Asabar, Natasha ta tabbatar da cewa ta yi aiken sako ga Majalisar Dattawa game da batun dawowarta.
Ta ce, za ta yi hakan bisa hukuncin kotu da ya ba ta damar komawa bakin aiki, tana mai cewa ba hakan ba umarni ba ne, saidai hukunci ne.
Sanatar, wadda aka Dakta tun a watan Maris, ta ce dakatarwar bai hana ta gudanar da ayyuka a mazaɓarta ba, saidai ya kore mata ikon ɗaukar nauyin ƙudiri da miƙa bututuwa.
An dakatar da Natasha ne bisa zargin ta rashin biyayya, lamarin da lauyoyinta suke ƙalubalanta a kotu.
A wani hukunci da aka yi kwanan nan a wata kotu, an ayyana dakatarwar da aka yi matq a matsayin haramtacce, wanda majalisar ƙalubalanta a wani ƙara da ta ɗaukaka, lamarin da sanatar ta ce ba zai hana ta komawa ba.
