Gwamna Raɗɗa ya tsallake wani mummunan hatsarin mota a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya gamu da hatsarin mota a lokacin da ayarin motocinsa ke tafiya a kan hanyar Daura zuwa Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa wata motar ‘yan kasuwa ƙirar Golf ce ta yi taho mu gama da motar da gwamnan ke ciki lamarin da ya sa gwamna Raɗɗa ya samu rauni a ƙafarsa.

A cikin wata sanarwar da kakakin gwamnan, Ibrahim Mohammed Kaula ya fitar, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce gwamnan bai ji wani mummunan rauni ba sakamakon hatsarin.

Sanarwar ta ce gwamna Raɗɗa ya yi godiya ga Allah (S.W) da ya tsare shi daga hatsarin ya kuma gode wa al’ummar Jihar Katsina gami da ‘yan uwa da abokan ar’ziki da suka aike da saƙon jajantawa.

By ukarofi