Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan naɗin ɗaya daga cikin mutanen ta kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Alh. Sanusi Garba Rikiji a matsayin Babban Darakta na Ofishin Tattaunawa Kan Kasuwanci na Najeriya (NOTN).
Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da jami’in sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar Yusuf Idris ya rabawa manema labarai, ya bayyana naɗin da shugaba Tinubu ya yi a matsayin wata manuniya da ke nuna ƙauna da amincewar da shugaban ƙasa yake da shi a Jihar Zamfara da al’ummarta.
“Jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Hon Tukur Umar Ɗanfulani ta yi alƙawarin ci gaba da biyayya ga shugaba Tinubu da dukkan kyawawan tsare tsaren gwamnatin sa da ƙoƙarinsa na kawo sauyi ga Nijeriya”.
“A yayin da muke taya sabon wanda aka naɗa murnar wannan ci gaba a rayuwarsa, muna kira gareshi da ya cigaba da zama abin koyi a kowane lokaci a matsayinsa na jakada nagari a Jihar Zamfara. Sanarwar ta bayyana.
A cewar sanarwar, jam’iyyar na da ƙwarin gwiwar cewa Sanusi Garba Rikiji zai tabbatar da inganta sabon ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen sauya tushen cinikayyar ƙasar nan ta hanyar sabbin dabaru masu cike da hangen nesa da cigaban tattalin Arzikin Nijeriya”.
“Muna kira a gareshi, ya jajirce ta fannin samar da hanyoyin da za a bi don magance matsalolin tattalin arzikin ‘yan ƙasa da kuma nasarar cigaban shugaba Tinubu.” A cewar sanarwar
