19
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya kirayi al'ummar ƙauyuka sama da guda 2,000 dake kusa da rafuka da wuraren da ke da barazanar ambaliya da su ƙaura zuwa yankuna masu tudu. Bago ya yi wannan kira ne a wata takarda ta hannun ofishin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Jonathan Vatsa, ranar Juma'a. Ya ce, akwai buƙatar al'ummar da ke ire-iren yankunan ylsu kiyaye gargaɗin Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa game da yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwan sama a wasu yankunan faɗin Nijeriya. A kwanakin baya ne hukumar ta yi…
