18
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana yadda wasu ƴan gaban goshi suka riƙa yin kutsen takardu kai-tsaye duk da tsarin bi ta ofishinsa da doka ta wajabta. Farfesa Gambari, wanda ya yi aiki a muƙamin daga shekarar 2020 zuwa 2023, ya bayan haka ne a yayin hira da gidan telebijin na Channels, ranar Juma'a. Ya ce, masu yin hakan a lokacin suna amfani da damar ganawa da shugaban ƙasar ne kai-tsaye, lamarin da acewarsa ya sa suka riƙa miƙa masa takardun.…
