Yanzu-yanzu: Tinubu ya maye gurbin UniMaid da sunan Muhammadu Buhari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya sake wa Jami’ar Maiduguri suna, inda ya sanya mata sunan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Shugaban Ƙasar ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, yayin Zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka faɗaɗa don karrama tshohon shugaban a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.

Daga yanzu, za a riƙa amfani da “Muhammadu Buhari University’ a matsayin sunan jami’ar.

Zaman ya samu halartar ƴaƴan tshohon shugaban ƙasar duba da gayyata ta musamman da suka samu daga fadar shugaban ƙasar.

By Babaji