Babaji

5698 Posts

Buhari: Shettima, Atiku, Obi, Zulum, El-Rufa’i da wasu sun halarci addu’ar uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Da dama daga cikin manyan ƴan siyasa da masu alfarma ne suka taru a garin Daura a ranar Laraba, domin halartar addu'ar Fidda'u ga marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a wani asibiti dake Landon. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya jagoranci tawagar, wadda ta haɗa da Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda da Babagana Umara Zulum na Borno inda aka yi wa mamacin addu'o'in neman samun rahamar Allah. Suaran sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar; tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa…
Read More

Fethullah: Gwamnatin Turkiyya ta yi gargaɗin ɓullar sabuwar ƙungiyar ƴan ta’adda a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin ƙasar Turkiyya ta yi gargaɗin cewa akwai mambobin wata ƙungiyar ta'addanci da ake kira da 'Fethullah' a Nijeriya, waɗanda ke ayyukansu a ƙasar da wasu ƙasashe. Jakadan ƙasar ga Nijeriya, Mehmet Poroy ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja, lokacin shagalin Ranar Dimukraɗiyya da Haɗin kai ta ƙasar. Ambasada Poroy ya ce, akwai wata tawaga da ta yi yunƙurin juyin mulkin a Turkiyya a ranar 15 ga Yulin 2016, wanda ba a cimma nasara a kai ba, lamarin da aka zargi mayaƙan FETO da ƙaddamarwa. Daga lokacin ne aka riƙa kama mambobin ƙungiyar…
Read More

Buhari: RTEAN ta kirayi mambobinta su yi addu’a ga marigayi tsohon shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Ma'aikatan Sufurin Motoci ta Ƙasa (RTEAN) ta yi alhinin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata. Shugaban ƙungiyar, Dakta Musa Muhammad Maitakobi a wata takarda, ya yi jimamin rashin marigayin Shugaban, wanda ya bayyana a matsayin jagora na gari mai ƙoƙarin riƙo da gaskiya bisa jajircewa da sadaukarwa ga al'ummar ƙasa. Ya kuma ce, Buhari mutum ne da ya kasance mai kishin ƙasa kuma jagora abin koyi wajen tsayuwa akan hidimta wa ƙasa da al'umma, yana mai cewa za a cigaba da tunawa da shi…
Read More

An binne gawar marigayi Janar Muhammadu Buhari a gidansa dake Daura a Jihar Katsina

Jana’izar marigayin ta samu halartar Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, shugaban ƙasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló, da Fraministan Ministan Jamhuriyar Nijar, Ali Lamine Zeine. Sauran manyan baki sun haɗa da shugabannin rundunonin tsaro, shugabannin masana’antu, Ministoci, tsofaffin gwamnoni, wakilin shugaban ƙasar Chadi, malamai, da fitattun mutane daga cikin gida da waje. Kafin binne gawar, dakarun haɗin gwiwar sojoji sun gudanar da harbe-harben ban girma sau 21 a matsayin girmamawa ta ƙarshe ga marigayin. Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, shi ne ya karanta tarihin rayuwar Buhari a taron, inda…
Read More

An yi jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Imam Hassan Yusuf na babban masallacin garin Daura ya jagoranci Sallar jana'izar a filin jiragen sama na Choppers da misalin ƙarfe 4:56 na yamma. Gwamnatin Katsina ta gina wannan filin ne a lokacin da marigayi Muhammadu Buhari ke shugaban kasa. Tun da misalin ƙarfe goma na safe jama'a musamman ƴan yankin Daura da manyan baƙi daga sassa daban-daban suka fara tururuwa zuwa gidan marigayi Muhammadu Buhari, inda wasu kuma suka isa filin da aka gudanar da jana'izar. Shugaba Bola Ahmad Tinubu wanda ya samu rakiyar ɗansa Seyi Tinubu da Gwamna Dikko Raɗɗa suka tarbi gawar…
Read More

Gidauniyar ‘C&C Friends Foundation’ ta yi jimamin rasuwar Buhari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gidauniyar abokai ta 'C&C Friends Foundation' ta bayyana kaɗuwarta game da rashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata. Marigayin, ya rasu ne a wani asibiti dake Landon bayan shafe shekaru 82 a duniya. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta na ƙasa, Sanusi Garba Kalambaina, gidauniyar ta miƙa gaisuwar ta'aziyyarta ga Shugaba Bola Tinubu, iyalan marigayin, gwamnatin Katsina da al'ummarta gami da ilahirin ƴan Nijeriya. Ta kuma yaba wa jajircewa da ƙoƙarinsa wajen samar wa Nijeriya ci-gaba a fannoni da dama tare da…
Read More

Wanda ya yi yunƙurin kashe ni ya tafi ya bar ni a raye – Sunday Igboho kan rasuwar Buhari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai fafutukar kafa ƙasar Yarbawa, Sunday Adeniyi da aka fi sani da Sunday Igboho ya magantu game da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana a matsayin "babban mai laifi" da ya taɓa yunƙurin halaka shi. A ranar Lahadi ne shugaban Nijeriyar ya rasu a wani asibiti dake Landon bayan wani gajeren rashin lafiya. A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, an ga yadda Igboho ya ke bayanin yadda tsohon shugaban ƙasar ya umarci jami'an DSS su je gidansa da tsakar dare. Ya yi ikirarin cewa an yi hakan ne…
Read More

Yadda babbar ƴar Buhari, Fatima ta fashe da kuka yayin da suka isa wajen jana’iza

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ana cigaba da jimamin rashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yau Talata, yayin da iyalansa ƙarƙashin jagorancin Fatima Buhari suka je wajen jana'izar a Daura. An ga yadda Fatima ke zubar da ƙwalla a lokacin da ta isa gidansa dake garin, inda a nan ne za a yi jana'izar. Haka kuma an ga yadda makusantanta suke lallashin ta yayin da suke tarbar su. Sannan, gabannin haka ne sauran iyalan suka isa birnin domin gudanar da shirye-shiryen jana'izar. A safiyar yau ne gawar ta bar Landon zuwa Nijeriya, wadda za a yi jana'izarta da…
Read More

Jonathan da tsohon shugaban Ghana sun ziyarci makusantan Buhari a Landon

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Johnathan da tsohon shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo suka ziyarci Kashim Shettima da tawagarsa a Landon a yayin jimamin rasuwar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Mai taimaka wa Mataimakin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya bayyana hakan a wata takarda. Ya ce, iyalan marigayin sun shaida cewa ya rasu ne bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci, da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi, a wani asibiti dake Landon. A ranar 28 ga watan Yuni ne marigayin ya yi…
Read More