
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai sharhi akan harkokin siyasa, Farfesa Farooq Kperogi ya yi zargin cewa marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da matarsa A’isha sun rabu a matsayin ma’aurata cikin sirri kafin ya rasu.
A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025 Buhari ya rasu a wani asibiti dake Landon, Ingila.
An yi masa jana’iza ne a ranar Talata, a gidansa dake mahaifarsa ta garin Daura a Jihar Katsina.
Farfesa Kperogi a wani saƙo da ya wallafa ta Facebook, ya yi zargin an samu saki a tsakanin Buhari da A’isha tun da jimawa kafin rasuwarsa, lamarin da a cewarsa ya sa ta koma amfani da Aisha Halilu.
Ya kuma ce, mutane sun yi ta yaɗa cewa tshohon shugaban ƙasar ya nemi Aisha da ta nema masa yafiyar al’ummar Nijeriya, inda ya ce bai tabbatar da ingancin maganar ba domin ba a matsayin mata da miji suke ba kafin ya rasu.
Sannan, ya ce a lokacin da Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa ya koma Daura, ba sa tare da ita. Haka ma da ya koma Kaduna.
A cewar Farfesan, ko da jikin tsohon shugaban ƙasar ya yi tsanani a Landon, da fari ta ƙi amince wa zuwa inda ya ke kasancewar ta ɗauki kanta a matsayin wadda ba matarsa ba, lamarin da ya sa sai dab da rasuwarsa sannan ta je inda ya ke.
Ya ƙalubalanci matsayin da ta yi amfani da shi a yayi jana’izar marigayin, inda ya ce duk abinda ta yi ta yi su ne a matsayin bazawara.
A shekerar 1989 ne Buhari ya auri Aisha inda suka haifi ƴaƴa biyar da suka haɗa da Zahra, Yusuf, Halima, Amina, da Aisha.
Tsohon shugaban mulkin sojin yana da wasu ƴaƴa biyar da matarsa ta farko marigayiya Safinatu Yusuf.
