Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar al’umma Manhaja.
Kamar dai yadda muka soma, a satin da ya gabata, mun faro darasin mu kan abinda ya shafi kwalliya, inda muka bayyana muhimmancin ta ga mata.
A wannan makon ma za mu ci gaba ne daga darasin farko.
A rayuwa, kafin mace ta buɗe baki, jikinta da fuskarta sun riga sun faɗa wa duniya wani abu. Tsarinta, tsaftarta, da kwalliyarta na iya zama tamkar wasiƙar da ba a rubuta ba, amma duk mai hankali zai karanta.
A cikin birane har ma da karkara, kwalliya ta wuce a kalla a matsayin ado. Ta zama alamar da ke nuna shiri, daraja da kula da kai. Mace mai shirya kanta ba kawai tana neman yabawa ba ce, tana bayyana cewa ta damu da kanta, tana girmama halittar da Ubangiji ya ba ta.
Mun kai lokacin da aka mayar da kayan ado abin dole ko kuma in ce aka sa su a layin kayan buƙatu na rayuwa, kamar abinci da sauransu. Akwai lokacin da abin ado ke zama tamkar abin buƙata. Wanda har ta kai ake ganin idan mace ta ƙi kwalliya tamkar tana ƙoƙarin fitar da kanta a layin mata ne.
Duk da cewa kwalliya ba ta zama abin aibu ba, amma tasirin ta a wannan zamanin ya sa mata da yawa ke rena kamannun da Allah ya yi masu, har suke ganin idan ba da kwalliya ba ba za su ganu, ko su zama abin birgewa ga wasu ba.
Wannan dalilin kawai ya jefa mata da dama a hatsari, wanda kamar yadda darasinmu na can baya kan bilicin ya bayyana, tasirin haske tsakanin al’ummarmu ke jefa mata da yawa a hatsarin bilicin ido rufe.
Wannan ne ya sa mata da yawa suke bautawa kayan ƙawa, wanda ba a nan matsalar take ba, akan samu wasu kayan kwalliya da ba su da inganci, saidai suna ba fuska sheƙi, don haka sai idonsu ya rufe daga ganin aibun da ke tare da su har sai wani abu ya samu fatar.
A cewar Dakta Ibrahim Adamu daga UNN Nsukka: “Idan mata suka ci gaba da amfani da sinadarai masu guba, ba wai kawai za su lalata fatarsu ba ne, har da yiwuwar kamuwa da cututtuka masu hatsari a jiki.”
