Daga AISHA ASAS
‘Uwa ce ke koya wa ɗiyarta zama karamar mace kafin ta zama uwargida’
A rayuwar baya, uwa ce malamar ‘yarta. Ita ke koya mata riƙo da addini, tsafta, kunya da ladabi da biyayya. Ita ke yi mata lalle, tana ɗinke mata duk wata ɓarakar gidan aure tun kan ta shige ta, tana ba ta shawarar rayuwa. Amma a yau, akwai iyaye mata da ‘ya’yansu mata da ba su iya zama tare fiye da minti goma ba tare da gardama ba. A wasu gidaje, uwa ba ta san abokiyar ‘yarta ba, ko irin saƙonnin da take karantawa a wayar ta ba.
A wannan makon shafin Iyali na jaridar al’umma Manhaja, zai karkata kan duba yadda uwa za ta gina alaƙa mai ƙarfi da ‘yarta mace, domin kareta daga rushewar tarbiyya da gurɓataccen tunani.
A irin yadda zamani ya koma a yau, yarinya na neman wanda za ta faɗa wa damuwarta, idan ba uwa ba ce, to sai abokiyar banza ko saurayi. Wannan ne ke haifar da bijirewa, ɓoye gaskiya, lalacewar tarbiyya da rashin kunya. Wanda za mu iya cewa, ba lokacin da ‘ya mace ta fi buƙatar uwa kamar wannan zamani da muke ciki.
Kafin mu yi nisa, shin wacce ce uwa a rayuwar ‘yarta?
1. Ita ce ginshiƙi da kariya: ‘Ya mace tana buƙatar mai riƙe mata sirri da fahimtar inda ta dosa.
2. Ita ce mai koya mata darajar jikinta da kamun kai.
3. Ita ce za ta faɗa mata gaskiya game da rayuwa, jima’i, aure da nauyin zama mace.
4. Ita ce abokiyar shawara, mai karɓar kuka da dariya.
Idan mun koma ɓangaren yadda ita uwa za ta gina kyakkyawar alaƙa da ‘yarta da har za ta iya sakin jiki sosai da ita. Za mu iya cewa akwai hanyoyi da dama, daga cikinsu akwai:
1. Zama da ita lokaci zuwa lokaci don yin wasa da dariya, ba da tsangwama ba, ko kama ta da laifin abinda ta faɗa.
2. Faɗa mata gaskiya game da abubuwan da ke gaban mace: jinin al’ada, halayyar samari, da darajar aure.
3. Koya mata sana’a ko fasaha, kamar lalle, ɗinki, girki da sauransu.
4. Rungumar ta idan tana cikin damuwa, kar a dinga zagi ko nuna ƙiyayya.
5. Bayar da misali da hali, uwa ta zama abin kwaikwayo ta kwarai.
6. Hana ta fita da shiga ta banza, ta hanyar lurar da ita aibun hakan.
7. Kare ta daga faɗawa cikin soyayya kafin lokaci, ta hanyar fahimtar da ita illolin hakan da zubewar mutunci.
.
