A kan ran Bayahude ɗaya an kashe Falasɗinawa 450!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Shin me ribar dakatar da yaƙin Gaza? Tambaya ce da na ke ganin ta na da muhimmanci don an ce ina amfanin baɗi ba rai. A gurguje ma zan ce akwai amfani ga sauran mutanen da ba a gama kashewa ba tun da mai rabon ganin baɗi ko a na mazuru a na shaho sai ya gani da yardar Allah. Yanzu dai ƙarfin a samu tsagaita wutar na zuwa daga masu rowan wutar ne da alama ke nunawa sun riga sun cimma burin su na ragargaza Gaza. Duk labarun su ke bayarwa cewa ‘yan Hamas sun kashe mutum 1200 a kutsen da su ka yi yankin Isra’ila a 7 ga Oktobar 2023 don haka za su murƙushe Hamas. Zuwa yanzu sun kashe fiye da Falasɗinawa 50,000 ciki kuwa mafi yawa mata ne da ƙananan yara. Idan ramuwa ce kun ga a kan kowane Bayahude daya an kimanin kashe Falasɗinawa 450! Kuma kisan ba an daina ba ne kusan kullum sai an kai hare-hare Gaza an kashe mutane wasu ma sun samu sun kwanta su na barci sai dai su wayi gari a lahira. Fahimtata jinin Falasɗinawa ba shi da daraja a idon manyan masu juya siyasar duniya. Ga hotunan da mu ke gani na yara ƙanana an kashe su iyayen su na kuka amma an jima ko gobe ba zai sa a fasa kai wani harin a kashe wasu ba. Hare-haren nan har kan asibitoci inda masu jinya na kwance a asibiti za a jefa bom don kashe su gaba ɗaya. Hakanan za a riƙa gigita al’ummar Gaza yau a ce su koma kudancin Zirin gobe a ce ba a son ganin su a can ɗin ma. Wasu sun kafa tantuna su na zaune ba su tsira ba sai an jefa mu su bom. Wannan gaskiya kisan ƙare dangi ne. In a na maganar Hamas, a yanzu duk an kashe shugabannin Hamas da a ka sani kama daga Isma’ila Hanieh zuwa Yahaya Sinwar. Idan Isra’ila na zargin Hamas na yin mafaka da fararen hula, to kakaf mutan Gaza ma su nawa ne? me ya sa za a jefa bom kan mai uwa da wabi alhali sojojin Isra’ila na shiga ko ina a Gaza su yi abun da su ka ga dama. Tun wannan hari na 2023 shin wani hari kuma Hamas ta sake iya kai wa cikin Isra’ila? Kazalika a ina ’yan Hamas za su zauna tun da su ƙungiya ce ba kamar sojojin Isra’ila masu jiragen yaƙi da tankunan yaƙi da gingima-gingiman boma-bomai ba. A kwanakin baya ma har wasu mazuna Gaza sun yi zanga-zanga da ke buƙatar ‘yan Hamas su fice daga yankin ko gaba ɗaya su kunce ɗamarar yaƙi da tunanin hakan zai sa Isra’ila ta daina jefa mu su boma-bomai. Idan Isra’ila ta tashi hari ba ta ware waye marar ƙaunar Hamas waye mai goyon bayan Hamas kan kowa kawai ta ke jefa makamai. Indai mutum Bafalasɗine ne to tamkar Isra’ila ta yanke ma sa hukuncin  kisa sai jiran lokacin zartarwa. Ko su kan su shugabannin ƙasar Hamas a Ramallah ba su tsira daga cin zarafin Isra’ila ba. Yankin yammacin kogin Jodan ma da’irar zubar da jinin Falasɗinawa ne. Duk lokacin da a ka kawo batun kafa ƙasar Falsɗinu mai ‘yanci sai Isra’ila ta sa kafa ta shure yunƙurin yayin da Majalisar ɗinkin Duniya ba ta da kataɓus don Amurka za ta hau kujerar na ki. Duk kalaman nuna takaici na sakataren Majalisar ɗinkin Duniya kan zama tausayawa don sai Amurka ta amince a kujerar iya hawa kujerar na ki a kwamitin tsaro. Tsarin kwamitin tsaro mai ƙasashe 15 da masu dindindin ba adalci a ciki kuma a kan samu kusan duk ƙasashen sun dau matsaya ɗaya ta ɗaukar mataki kan Isra’ila amma caraf sai Amurka ta biris da matsayar. Amurka dai ba za ta ga laifin Isra’ila ko da kuwa za ta kashe dukkan Falasɗinawa ne.

ƙungiyar Hamas mai mulkin Zirin Gaza na buƙatar tabbacin sabuwar yarjejeniyar da a ke sa ran kullawa don tsagaita wuta ta haɗa da dakatar da yaƙi gaba ɗaya.

Wannan kazalika na zuwa ne a lokacin da Isra’ila ta sake kai hare-hare a sassan Gaza da mutane da dama su ka rasa ran su.

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta fidda adadin alƙaluman da ke nuna kimanin mutum 59 ne su ka rasa ran su a Alhamis ɗin makon jiya sanadiyyar hare-haren sojojin Isra’ila.

Isra’ila na cewa akwai alama mai ƙarfi ta cimma tsagaita wuta da batun miƙawa Isra’ila kamammun da Hamas ke garkuwa da su a yaƙin da ya kai wata 21.

Yunƙurin samar da tsagaita wuta a Gaza ya ƙara ƙarfi biyo bayan shigewa gaba da Amurka ta yi wajen samar da tsagaita wuta a hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran da ya haddasa yaƙi na tsawon kwana 12.

Dama batun kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya ne kan zama abun da ba a cimmawa a yerjeniyoyin baya.

A na tsammanin cikin mutum 50 da Hamas ke garkuwa da su, 20 na raye kuma yarjejeniyar na buƙatar miƙa masu ran da matattun da hakan zai kai ga sako wasu Falasɗinawa da ke garkame a gidajen yarin Isra’ila.

Hamas ta bayyana karsashin neman tsagaita wuta tsakanin ta da Isra’ila a yaƙin da ya shiga wata na 21.

Wannan na zuwa biyo bayan zagin da Amurka ta yi kan shirin tsagaita wuta da masu shiga tsakani su ka gabatar.

ƙungiyar ta Hamas da ke mulkin Gaza ta bayyana matsayar bayan ganawa da takwarorin ta a gwagwarmaya da su ka haɗa da ISLAMIC JIHAD wacce ke son tabbacin yarjejeniyar za ta dakatar da yaƙin gaba caya kar ya zama daga bisani Isra’ila ta cigaba da farmaki bayan miƙa ma ta kamammun mutanen ta.

Rahotanni sun bayyana kashe ƙarin mutum 20 a Gaza a sabbin hare-haren Isra’ila ranar asabar kuma Isra’ila ba ta yanke matsaya ba ta ƙarshe kan yarjejeniyar.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci fadar White House don tattaunawa da shugaba Trump kan yarjejeniyar.

Donald Trump a amsa tambaya kan matsayar ta Hamas ya nuna akwai buƙatar yin wani abu kan Gaza.

Trump ya gana da Firaministan Isra’ila a fadar White House kan shirin neman tabbatar da tsagaita a yaƙin Gaza.

Trump ya zauna kan dogon teburi ɗaura da Netanyahu ya na mai nuna lokaci ya yi na dakatar da yaƙin Gaza da nuna Hamas na shirye don ƙulla yarjejeniya.

Donald Trump wanda a baya ya nemi al’ummar Gaza su tattara komatsen su, su fice daga Zirin, yanzu ya nuna za a iya samun tsagaita wuta zuwa mako mai shigowa.

A nan Netanyahu ya ce Isra’ila ba za ta kyale Gaza ba tare da zuba ido na tsaro ba kuma sam ba su damu da tunanin mutane da za su iya cewa ai hakan ya tauye matsayar zaman Falasɗinu a matsayin cikakkiyar ƙasa mai ‘yanci.

Wani abun dubawa ma shi ne Netanyahu ya zaɓi da a ba wa Trump lambar yabon nan mai daraja ta duniya NOBEL kan abun da ya ce aikin sulhun zaman lafiya da ya ke jagoranta a ƙasashe.

Netanyahu ya miƙa wa Trump kofin wasiƙar da ya turawa kwamitin NOBEL kuma dama Trump na da burin samun wannan lambar.

Mutane sun taru daf da fadar White House a lokacin ganawar su na caccakar Netanyahu da zama mai kisan ƙare dangi a Gaza.

Wani sabon harin Isra’ila kan sassa daban-daban na Gaza ya yi sanadiyyar kisa ga kimanin Falasɗinawa 40.

Asibitin Al-Nasr da ke yankin Khan Younis a kudancin Gaza ya bayyana cewa cikin waɗanda hare-haren su ka kashe akwai mata 17 da yara 10.

Wani abun tausayi ma a wannan sabon harin akwai mutum 10 rus da su ka rasa ran su daga iyali ɗaya.

Sojan Isra’ila ba su ce komai ba kan wannan mummunan harin in ka deɓe bayyana cewa sun kai hari hari kan fiye da bigirori 100 da su ka auna waɗanda zayyana da ‘yan bindiga, rumbunan makaman Hamas da hanyoyin hada-hada na ƙarƙashin ƙasa.

Firaministan Isra’ila duk da waɗannan kashe-kashe ya sake ganawa da shugaban Amurka Donald Trump kan batun tsagaita wuta da hakan zai iya kai wa ga dakatar da yaƙin da ya kai wata 21.

Masu shiga tsakani na cigaba da tattaunawa yayin da mazauna Gaza ke fatar dakatar da yaƙin da ke ɗaukar rayukan jama’a kusan kullum.

Da alamun Isra’ila na son yin iyakacin kisan da za ta iya yi don ko an tsagaita wuta ta riga ta murƙushe al’ummar yankin da sunan gamawa da Hamas.

Trump da Nartanyahu sun zauna a ginin Capitol su ka shaidawa manema labaru burin su na murƙushe Hamas da kuma kasancewar zumuncin Amurka da Isra’ila ya fi kowane lokaci ƙarfi wajen fahinmtar juna a shekaru 77.

Hakanan Netanyahu ya kawo batun nan na inganta hulɗar ƙasashen Larabawa da Isra’ila  ABRAHAM ACCORD da Trump ya ƙirƙiro a mulkin sa na farko har da burin ƙarfafa diflomasiyya tsakanin Isra’ila da Saudiyya.

Turkiyya da ta ke ƙasar Turawa a lokacin ta soki ƙasashen Larabawa da su ka shiga wannan diflomasiyya da su ka haɗa da Daular Larabawa da Katar da zayyana hakan da abun takaici.

Hakanan shi ma shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya nuna matuƙar fusata da abun da Larabawa su ka yi, ya na ɗaukar hakan da tamkar ’yan uwan su sun yi biris da su.

KAMMALAWA

Wani lokaci cikin mako jakadan Trump na gabar ta tsakiya Steve Witkoff zai sauka a Doha na Katar don cigaba da zantawar bayan fage tsakanin Isra’ila da Hamas. Shin muhukuntan Doha da na Alkahira za su iya matsa lamba a samu tsagaita wuta ta gaba ɗaya ba tare da la’akari da diflomasiyyar su ta ƙud da ƙud da Amurka ba da ke son al’ummar Gaza su fice daga ƙasar su ta gado inda Isra’ila ke sha’awar maida Zirin sansanin sojan ta

By ukarofi