20
Jun
DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Gwamnatin jihar Nasarawa tace zata cigaba da tsare tareda hukunta masu haƙar ma'danai ba bisa ka'ida ba a jihar.Kwamishinan ma'aikatan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar honorabul Kwanta Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattauna da manema labarai a ofishin sa dake Lafia. Yace ba shakka hakan haƙƙi ne daya rataya a wuyar gwamnatin jihar ta tabbatar tana kare duka ma'adanai da sauran kaddarorin jihar musamman Idan akayi la'kari da yadda wasu Ke shigo jihar daga wasu jihohin daban don haƙar ma'adanan ba bisa ƙa’ida ba Kuma basa karban lasisin aikin.…
