Yadda wasu ke sayen fetur a Nijeriya suna sayarwa kan N1700 a Jamhuriyar Benin

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An nuna damuwa game da yadda ake fasa ƙwaurin man fetur a tsakanin ƙasashen yammacin Afirka da ke makwabtaka da Nijeriya kamar su Jamhuriyar Benin, Kamaru, da sauransu.

Farashin man fetur a Nijeriya ya kai kusan Naira 701 a kowace lita yayin da ake sayar da shi kan 1,700 a wasu ƙasashen yammacin Afirka. Wannan bambamcin farashin ya haifar da ƙaruwar masu fasa ƙwaurin fetur ɗin daga Nijeriya cikin makonni biyu da suka gabata.

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Yola. 

Ya bayyana cewa, dole ne hukumar da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro su haɗa kai don yaƙar wannan barazana.

Ya ce, “A yau, mun zo ne domin sanar da jama’a irin dabarun da hukumar kwastam ta Nijeriya ke yi wajen magance matsalar fasa-ƙwaurin man fetur ta hanyar ‘Operation Whirlwind’ da aka ƙaddamar kwanan nan, ƙarƙashin kulawar ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

“Kimanin shekara guda da ta wuce, Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar cire tallafin mai. Wannan muhimmin mataki na da nufin ’yantar da maƙudan kuɗaɗe da za a iya saka su zuwa wasu sassa masu albarka na tattalin arziki, da rage matsin lamba kan asusun ajiyar mu na musaya na ƙetare, da haɓaka cigaban tattalin arziki.

“Tasirin nan da nan ya kasance daidaitawa sama da farashin man fetur don nuna gaskiyar halin da ake ciki. Duk da hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsalar kuɗi ga magidanta, musamman masu ƙaramin ƙarfi, bincike ya nuna cewa farashin mai a Nijeriya ya kasance mafi arha idan aka kwatanta da sauran ƙasashen yankin yammacin Afirka da Afirka ta Tsakiya,” inji shi.

Da yake ƙarin haske, Adeniyi ya ce, “Yayin da ake sayar da fetur a kan Naira 701.99 a Nijeriya, ana sayar da shi a kan Naira 1,672.05 a Jamhuriyar Benin da kuma Naiea 2,061.55 a Kamaru. A sauran ƙasashen yankin, farashin fetur ya tashi daga N1,427.68 a Laberiya zuwa N2,128.20 a Mali, wanda ya kai N1,787.57, bisa ga bayanan farashin man fetur da aka samu.”

Shugaban Kwastam ɗin ya ce wannan kwatankwacin fa’idar farashin, duk da cewa yana da amfani ga ’yan Nijeriya, amma abin takaici, ya haifar da wani gagarumin safarar fetur daga Nijeriya, inda farashin ya ninka sau biyu zuwa uku.

Ya ce, rahoton ya tabbatar da hakan ne a kan wasu mutane na kwashe fetur a kowace rana zuwa jihohi daban-daban na Nijeriya, wanda aka samu daga Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya.