Ranar Dimukraɗiyya: Me ‘yan Nijeriya suke wa murna?

Spread the love

Ranar 12 ga watan Yuni muhimmiyar rana ce a tarihin Nijeriya, kasancewarta ranar da aka gudanar da Babban Zaɓen Shugaban ƙasa na shekarar 1993, wanda daga baya gwamnatin mulkin soja ta lokacin ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke, bisa zargin an tafka maguɗi. Wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka ya haifar da rabuwar kai mai tsanani a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman a ɓangaren kudanci da arewacin. 

Tun daga wancan lokacin alaƙar Kudu da Arewa ta cigaba da fuskantar ƙalubale, musamman a siyasance. Sakamakon yadda ƙabilar Yarabawa da ke zaune a Shiyyar Gabashin Nijeriya ke kallon ‘yan Arewa ne suka yi kaka gida a mulkin ƙasar. A saboda haka ne ma gangamin sake fasalin tafiyar da mulkin Nijeriya ya samu gagarumin tasiri, wanda har ta kai a lokacin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo farkon zaɓaɓɓun shugaban ƙasa daga ɓangaren Yarabawa, a shekarar 2005 ya ba da damar shirya Babban Yaron Canza Fasalin Ƙasa, wanda a lokacin aka kira da National Political Reform Conference. 

Sai dai duk da haka, haƙar ‘yan kudu ba ta cimma ruwa ba, sakamakon jajircewa da wakilan ‘yan Arewa a taron suka yi kan wasu muhimman batutuwa da suka shafin cigaba da tafiyar da ƙasar a matsayin dunƙulalliyar ƙasa. Abin da zai baku mamaki shi ne, bayan komawar mulki ga hannun mutanen yankin kudu maso gabas, a 2023 wancan batu na neman sake gyaran fasalin ƙasa da neman komawa kan tsohon tsarin larduna, da samar da ƙwarya-ƙwaryar ‘yancin kai ga gwamnatin shiyyoyi, na sake kunno kai, zaurukan Majalisar Ƙasa. 

Waɗannan wasu muhimman buƙatu ne na mutanen wannan yanki da suke ganin ta haka ne kaɗai za su iya samun ‘yancin mulkin kansu yadda suke so, da ba su damar samar wa al’ummarsu abubuwa na cigaba. Sai dai a ƙoƙarin tabbatar da ganin wannan buƙata ba ta samu ba, shugabannin Arewa da ke kan madafun iko sun yi ta ƙoƙarin ganin sun rarrashi ɓangaren Yarabawa da alƙawarin wasu muƙamai masu tsoka, don su ajiye gabarsu a gefe, a zauna ƙarƙashin ƙasa ɗaya.

Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Manjo Janar Abdulsalami Abubakar, shi ya fara ayyana ranar 29 ga watan Mayu, don ta zama Ranar Dimukraɗiyya ta Ƙasa, kasancewarta ranar da ‘yan Nijeriya suka karɓi mulkin kasar a hannun su ƙarƙashin Jamhuriya ta 4, saboda har wa yau kuma ita ce ranar da ake rantsar da sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnati. Amma tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2018 ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni ta zama ita ce Ranar Dimukraɗiyya ta Ƙasa, yayin da 29 ga watan Mayu zai cigaba da zama ranar miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Wannan canji da aka yi a cewar manazarta an yi shi ne da nufin ƙara rarrashin ‘yan yankin kudu maso gabas, domin su daina kallon har yanzu ‘yan Arewa ba sa son su da mulkin ƙasar nan. Duk kuwa da damar da suke da ita na shiga zaɓe da neman a zaɓe su, a duk lokacin da harkokin zaɓe suka tashi. 

A cikin jawabin da ya gabatar wa ‘yan Nijeriya ta kafafen watsa labarai a Ranar Dimukraɗiyya ta bana, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana muhimmancin gwagwarmayar da tsofaffin ‘yan kishin ƙasa, da suka haɗa da gyauron ‘yan boko da ‘yan siyasa, waɗanda a baya suka nuna ƙalubalanci gwamnatocin baya game da soke wancan zaɓe na 12 ga watan Yuni, domin kare haƙƙin ‘yan ƙasa na zaɓar shugaban da suke so, da tabbatar da nasarar dimukraɗiyya a ƙasar nan. Mutanen da wasu daga cikin su har sai da suka tafi gudun Hijira a wasu ƙasashen waje na kimanin shekaru 6, saboda yadda gwamnatin tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha ta ɗauki abin da suke yi a matsayin tawaye da cin amanar ƙasa. 

Daga cikin mutanen da ya ambata, akwai Janar Alani Akinrinade, Farfesa Bolaji Akinyemi, Farfesa Wole Soyinka, Cif Ralph Obioha, Cif Cornelius Adebayo, Olisa Agbakoba, Femi Falana, Abdul Oroh, Sanata Shehu Sani, Gwamna Uba Sani, Chief Olu Falae, da tsofaffin shugabannin ƙungiyar NADECO, wato National Democratic Coalition, Cif Ayo Adebanjo da Cif Ayo Opadokun.

Waɗannan mutane na daga cikin mutanen da suka ja daga da gwamnatin mulkin soja na Janar Sani Abacha, sakamakon gwagwarmayar da suka yi ta dawowa kan tsarin Dimukraɗiyya, wanda daga baya bayan mutuwar Janar Abacha, Janar Abdulsalami Abubakar ya yi wa fursunonin siyasa da masu gudun hijira afuwa, aka kuma samar da tsarin da ya ba da damar kafa jam’iyyun siyasa da shiga zaɓe. 

Gwagwarmayar da mambobin ƙungiyar NADECO da sauran ‘yan Nijeriya suka yi a wancan lokacin ita ce ta sa tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta ayyana mayar da Ranar Dimukraɗiyya zuwa waccan rana, domin muhimmancin ta a tarihin siyasar Nijeriya. 

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, wacce riba ‘yan Nijeriya za su iya bugun ƙirji su ce sun samu a tsawon shekaru 25 ɗin da ƙasar ta yi ƙarƙashin mulkin farar hula na dimukraɗiyya? Masana da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum dai na ganin ko da ‘yancin da ’yan ƙasa ke da shi na kafa jam’iyyun siyasa da shiga duk wacce suke so, da tsayawa takara don neman goyon bayan jama’a, da ‘yancin zaɓen ɗan takarar da suke so, daga kowacce jam’iyya, shi ma cigaba ne sosai. Sannan tun daga 1999 da aka zaɓi Olusegun Obasanjo, ‘yan Nijeriya sun yi shugabanni daban-daban har guda biyar a jere ba tare da katsewa ba. Akasarinsu ma sun yi mulki ne na zango biyu. 

Kodayake a ganin manazarta irin su Ɓictor Daɓid da Hamza Yakubu, maguɗin zaɓe da cin hanci da rashawa, sun taimaka wajen gurgunta dimukraɗiyyar da ake ciki. Yadda ake samun wasu gurɓatattun ‘yan siyasa da jami’an gwamnati suna cin karensu babu babbaka, wajen satar dukiyar ƙasa, da yin ɗauki ɗora a lokacin zaɓe, da kuma yadda ake katsalandan cikin siyasar jam’iyyu, domin murɗe zaɓen fid da gwani da fitar da baragurbin ɗan takara. 

Sai dai abin takaici shi ne yadda a bikin tunawa da Ranar Dimukraɗiyya ta bana da aka yi, jama’a da dama ba su nuna farinciki da nuna murna da ganin zagayowar wannan rana ba. Abin da wasu ke dangantawa da halin matsin tattalin da ’yan Nijeriya ke ciki, sakamakon tsadar rayuwa, ƙalubalen tsaro, karyewar darajar Nijeriya. Don haka babu abin da za a yi murna da shi, domin irin azabar da ‘yan ƙasa ke fuskanta a wannan lokaci. 

Duk da haka dai ba za mu kasa sa ƙasarmu a cikin addu’a ba, da fatan samun sassauci kan halin ƙunci da jama’a ke ciki, samun shigabanni nagari da sarrafa dukiyar ƙasa cikin ‘yanci da daidaito, yadda kowane ɗan Nijeriya zai yi farinciki da kasancewar sa ɗan ƙasa.

By ukarofi