18
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Thomas Fuller, wanda ake yi wa laƙabi da "Mai lissafin tunani", ɗan asalin Afirka ne da masu satar bayi suka sace shi tun yana da shekaru goma sha huɗu, sannan suka sayarwa Turawa masu sayen bayi a shekarar 1724. Fuller yana da tsananin fikira wajen warware matsalolin lissafi da ka, kuma a cikin ƙanƙanin lokaci. Wata rana an tambaye shi, "daƙiƙu nawa ne a cikin shekara ɗaya da rabi" cikin minti biyu ya bada amsar cewa, "daƙiƙa miliyan arba'in da bakwai, da dubu ɗari uku da huɗu". Haka an taɓa tambayarsa; daƙiƙa nawa mutumin da ya…
