An tursasa ni auren wanda ba na so, jaruma Ini Edo kan mutuwar aurenta

Daga AISHA ASAS 

A karo na farko, fitacciyar jaruma Iniobong Edo Ekim, wadda aka fi sani da Ini Edo, ta buɗe cikinta kan lamarin aurenta da tsohon mijinta, inda ta bayyana takaicinta kan aminta da yin wannan aure da ta yi.

A wata tattaunawa da Chude Jideonwo, shahararriyar jaruma kuma mai shirya finafinai, Ini Edo, ta bayyana nadamar ta kan amincewa da ta yi ta auri mijinta wanda suka rabu.

Idan mai karatu zai iya kai tunaninsa shekaru baya, jaruma Ini Edo ta auri wani ɗan kasuwa da ke zaune a Ƙasar Amurka mai suna Philip Ehiagwina, a ranar 29 ga watan Nuwamba, na shekarar 2008, wanda auren ya yi ƙarkon shekara biyar, inda suka rabu a shekarar 2013.

Da take amsa tambayar dalilin da ya sa ta ce ta yi danasanin yin auren, jaruma a Masna’antar Nollywood Ini Edo, ta bayyana cewa, an tursasa ta auren wanda ba ta so, kuma tana da yaƙini a lokacin da ta yi na cewa, kuskure ne kuma ba abinda zai haifa mata ɗa mai ido ba ne.

“Na yi nadamar amincewa da na yi na yin aure, saboda ba hukuncin da ya kamata in bi ba ne,” inji ta.

Duk da haka ta bayyana cewa, ba ta taɓa yanke ƙauna ga aure ba ko bayan rabuwarsu, sai dai ta sawa ranta za ta yi auren ne kawai idan wanda ya cancanta ta aura ya zo.

Dangane da lamarin yadda ta haifi tilon ‘yarta, wato ba tare da aure ba ko ɗaukar cikin da kanta duk da cewa ‘yar tata jininta ce, Ini Edo ta bayyana cewa, ta yanke hukuncin ne sakamakon samun ciki da ta yi yana zubewa ba sau ɗaya ba, hakan ya sa ta nemi wadda zata iya renon cikin ba tare da matsalar zubewa ba, aka haɗa kwanta a kimiyyance aka dasa a mahaifar matar ta haifa mata jininta, wato ‘surrogacy’ a turance. 

“Ba ni da miji, don haka na yi tunanin me zai hana in samu ɗa nawa na kaina. Ko ina da miji ko ba ni da shi ba ni da zaɓin da ya wuce wannan, saboda dai ina son ɗan ya zama nawa a jini, kuma aka yi sa’a kwayakwaina na da lafiya, sai kawai na yi.”