Dafin magani ne sanadin mutuwar Mohbad – Rahoto

Daga IBRAHIM HAMISU 

Rahoton binciken gawar marigayi mawaƙi Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad, ya bayyana yadda dafin ƙwayoyin maganin da ya sha a matsayin dalilin mutuwarsa.

A cewa The Cable, gwajin gawar da guba da aka gudanar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas, ya nuna yiwuwar kamuwa da wata mummunan rashin lafiyar da zai iya zama barazana ga rayuwa ko kuma dafin maganin miyagun ƙwayoyi a matsayin abin da zai iya haifar da mutuwar Mohbad.

Rahoton ya bayyana cewa, asibitin ya ɗauko samfurin abubuwan da ke cikin marigayi mawaki Mohbad, na daga hanta, ƙoda da huhu. Sai kuma jini da suka ɗiba da kuma ƙasusuwa, domin a yi masa gwajin guba.

Sakamakon binciken ya nuna alamun ‘Diphenhydramine’, maganin hana yaɗuwar jini, a cikin jinin marigayi mawakin.

Antihistamines kwayoyi ne da ake amfani da su don magance rashin lafiya kamar matsalar ciwon ciki, mura, da damuwa, da kuma wasu curuta.

Hakazalika binciken ya yi ƙarin haske, inda ya bayyana cewa, yawan maganin da aka samu a jikin mawaƙin ba ya haifar da kisa ko kuma cutar da shi ko kuma ya kai ga mutuwarsa.

Baya ga haka, gwaje-gwajen sun kuma nuna wani rauni a hannun dama na Mohbad, baya ga alamun fara rubewa da gawar ta nuna, sakamakon tono ta da aka yi kwanaki takwas bayan binne shi.

A iya binciken ba a samu wani ƙwaƙƙwaran abinda za a iya dangantawa da mutuwar tasa na daga magani ko wani yunƙuri, saidai hasashe. 

Rahoton ya yi ƙarin haske kan lokacin da aka gudanar da binciken wanda ya bayyana cewa, abin lura ne, sakamakon ba a gudanar da binciken a kashe garin mutuwar ba, maimakon haka sai da gawar ta yi kwanaki takwas  a binne kafin aka gudanar da shi.

Mutuwar Mohbad na ɗaya daga cikin mutuwar da ta shahara tare da fusata mutane da dama, inda ake zargin wasu da hannu a kisan matashin mawaƙin, sakamakon haka ne waƙoƙinshi suka yi tashe fiye da lokacin da yake raye, kuma mutane da dama daga ciki har da mawaƙa ‘yan uwanshi suka yi gangamin newan a ƙwatowa mawaƙin haƙƙinsa ta hanyar binciken silar mutuwar tasa.

Da wannan ne a ranar 21/09/2023, aka bayar da umurnin tono gawar tasa don gudanar da bincike kamar yadda jama’a suka nema wanda ya yi daidai da kwanaki takwas bayan binne gawar.