ukarofi

12550 Posts
Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar NBC, ta tabbatar da hana hukumar cin tarar gidajen rediyo da talabijin

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar NBC, ta tabbatar da hana hukumar cin tarar gidajen rediyo da talabijin

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da wani yunƙuri da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta ƙasa (NBC) ta yi na soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya hana ta ci gaba da ƙaƙaba tara ga gidajen rediyo da talabijin. A hukuncin da alƙalan kotun suka yanke baki ɗaya a ranar Laraba, kotun ta bayyana ƙarar ɗaukaka ƙarar da NBC ta shigar a matsayin wadda ke da manyan kurakurai na doka, saboda haka ba za ta iya ci gaba da sauraron karar ba. Mai shari’a Jane Inyang, wadda ta…
Read More
2027: Idan na zama Shugaban ƙasa zan tattauna da ’yan bindiga – Peter Obi

2027: Idan na zama Shugaban ƙasa zan tattauna da ’yan bindiga – Peter Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Nijeriya Democratic Congress (NDC), Mista Peter Obi, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027, gwamnatinsa za ta rungumi tattaunawa da ’yan bindiga da sauran masu aikata ta’addanci da suka nuna aniyar ajiye makamansu da rungumar zaman lafiya, yayin da za a yi amfani da ƙarfin gwamnati wajen murƙushe waɗanda suka ƙi daina tashin hankali. Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin BlackBoɗ with Rufai Oseni, inda ya yi bayanin yadda yake shirin magance matsalar tsaro da kuma ƙarfafa haɗin…
Read More
Yadda aka sayar da jariri sabon haihuwa miliyan N2.5 a Legas — ’Yan Sanda

Yadda aka sayar da jariri sabon haihuwa miliyan N2.5 a Legas — ’Yan Sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta kama wani likita, ungozoma da kuma wasu masoya bisa zargin sayar da jariri sabon kan kuɗi Naira miliyan 2.5. A cewar majiyoyin ’yan sanda, mahaifiyar jaririn mai shekaru 28 da saurayinta sun yanke shawarar ba za su riƙe jaririn ba, inda suka fara neman waɗanda za su saya tun kafin a haife shi. Da farko an kai matar wajen wata ungozoma domin ta haihu. Sai dai ta samu matsala yayin naƙuda, lamarin da ya sanya aka garzaya da ita wani asibitin kuɗi da ke yankin Ikorodu, inda wani…
Read More
Kotu ta ba da umarnin kama Sowore kan rashin halartar shari’a

Kotu ta ba da umarnin kama Sowore kan rashin halartar shari’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kama ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, bayan ya kasa halartar shari’arsa da ake yi kan zargin aikata laifukan yanar gizo. Sowore na fuskantar tuhume-tuhume biyu da Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar a kansa, bayan ya wallafa wani saƙo a shafukan sada zumunta inda ya kira Shugaba Bola Ahmed Tinubu da “mai laifi” (criminal). A zaman kotun da aka ci gaba da yi ranar Talata, Sowore bai halarta ba, duk da cewa ya…
Read More
Rundunar ’yan sandan Kebbi ta cafke masu laifuka daban-daban, ta ceto mutane da daƙile hare-hare

Rundunar ’yan sandan Kebbi ta cafke masu laifuka daban-daban, ta ceto mutane da daƙile hare-hare

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara wajen kama mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da daƙile hare-haren masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da makami da kuma masu alaka da ƙungiyoyin ta’addanci a sassa daban-daban na jihar. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Umar M. Hadejia, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi a ranar Laraba. Ya ce nasarorin da aka samu sun biyo bayan sahihan bayanan sirri, bincike da kuma haɗin kan al’umma da…
Read More
Makomar Nijeriya na hannun matasa, amma dole a samar musu dama

Makomar Nijeriya na hannun matasa, amma dole a samar musu dama

Saƙon da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar a ranar Dimokuraɗiyya ga matasan Nujeriya ya cancanci zurfin tunani. Lokacin da ya buƙace su da su “ginu a nan, su ƙirƙira a nan, su yi aiki a nan, kuma su kaɗa wuri’a a nan,” ya tabo ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yau: ƙara yawaitar ficewar matasa masu ilimi, kuɗi da ƙwarewa zuwa ƙasashen waje domin neman ingantacciyar rayuwa. Furucinsa na cewa “Nijeriya ita ce gidanku kuma makomarku” ya kasance kira ne na kishin ƙasa da kuma ƙalubale ga matasa. Kusan dukkan ƙasashen da suka ci…
Read More
Sojoji sun bazama Katsina da Zamfara daƙile ta’addanci

Sojoji sun bazama Katsina da Zamfara daƙile ta’addanci

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sojojin Nijeriya sun bazama jihohin Katsina da Zamfara, don ci gaba da daƙile ayyukan ’yan bindiga, inda Rundunar Sojojin Sashe na Biyu a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma ta sanar da ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su tare da daƙile wani yunƙurin sace mutane da yin garkuwa da su a farmaki daban-daban da ta kai a yankunan jihohin. A cewar rundunar, nasarar ta samu ne sakamakon ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci, bincike da ceto domin murƙushe ayyukan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma. Cikin wata sanarwa da Jami’in…
Read More
Amsar tallafin tsaro daga waje yana da hatsari, inji DSS

Amsar tallafin tsaro daga waje yana da hatsari, inji DSS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta yi watsi da shirin da zai bai wa ƙungiyoyi da cibiyoyin ƙasashen waje damar tallafa wa ayyukan tsaro a Nijeriya ta hanyar wani Asusun Tallafi na Musamman, tana mai gargaɗin cewa irin wannan tsari na iya kawo cikas ga ikon ƙasa, tona sirrin ayyukan tsaro da kuma bai wa wasu ƙasashe damar yin tasiri a harkokin leƙen asirin Nijeriya. Hukumar ta bayyana matsayinta ne a ranar Alhamis yayin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri na Majalisar Wakilai ya shirya kan ƙudirin dokar kafa Asusun…
Read More
Yadda Atiku ya sa aka sari mahaifiyata a hannun ’yan ta’adda – Rarara

Yadda Atiku ya sa aka sari mahaifiyata a hannun ’yan ta’adda – Rarara

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Fitaccen mawaƙin siyasa a arewacin Nijeriya, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana cewa, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya janyo wasu ’yan ta’adda daban suka sari mahaifiyarsa, Hajiya Hauwau Adamu, a hannun ainihin waɗanda suka fara kama ta, kamar yadda ake sarar kaya a wajen cin kasuwa. Rarara ya yi bayanin hakan ne a cikin makon nan yayin da yake mayar wa fitaccen mawaƙin kudancin Nijeriya Daɓid Adeleke, wanda aka fi sani da Daɓido. Idan za a iya tunawa, a makon jiya Daɓido ya fito idon…
Read More
Allah ba azzalumin kowa ba ne, inji Diezani bayan kotun Birtaniya ta wanke ta

Allah ba azzalumin kowa ba ne, inji Diezani bayan kotun Birtaniya ta wanke ta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana cewa hukuncin da wata kotu a Birtaniya ta yanke na wanke ta daga zargin cin hanci ya kawo ƙarshen shekaru masu yawa na abin da ta kira “cin zarafi, suka da kuma tsangwama ba tare da adalci ba.” Rahotanni sun nuna cewa Kotun Southwark Crown Court da ke birnin Landan ta wanke Alison-Madueke daga dukkan tuhume-tuhumen cin hanci guda shida da ake yi mata, bayan alƙalan shari’a sun shafe sa’o’i suna nazari kafin su yanke hukunci. Hakan ya kawo ƙarshen wata shari’a da ta ɗauki…
Read More