ukarofi

12550 Posts
Fetur da sadarwa: Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin ƙin ƙara haraji

Fetur da sadarwa: Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin ƙin ƙara haraji

A daina biye wa jita-jita, inji Ma’aikatar Kuɗi Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi watsi da rahotannin da ke iƙirarin cewa, tana shirin ƙaƙaba sabbin haraji kan harkokin sadarwa da kayayyakin man fetur, bayan fitar da sabon rahoton tuntuɓar tattalin arziki na Asusun Lamuni na Duniya (IMF) kan Nijeriya. Gwamnatin ta bayyana irin waɗannan rahotanni a matsayin kuskuren fassara abubuwan da ke cikin rahoton, tana mai jaddada cewa ba sa wakiltar manufofinta ko alƙiblarta ta fuskar tattalin arziki. Ta kuma tabbatar wa da ’yan ƙasaR cewa, duk wani matakin haraji da za a ɗauka nan gaba za…
Read More
Matsalar tsaro: Gwamna Raɗɗa ya gana da sarakunan Katsina da Daura

Matsalar tsaro: Gwamna Raɗɗa ya gana da sarakunan Katsina da Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya gudanar da wani muhimmin taro da Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman, da Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, tare da hakimai da dagatai masu unguwanni daga sassa daban-daban na faɗin jihar. Taron ya haɗa manyan shugabannin na masarautun gargajiya domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi mulki, ci gaban al’umma uwa uba matsalar tsaro tare da mai da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masarautun gargajiya. Gwamnan ya bayana muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ƙarfafa haɗin kai, da kuma…
Read More
Poetic Wednesdays ta yi bikin cika shekaru 10 da fitar da jigo akan harsuna na taron KAPFEST na Uku

Poetic Wednesdays ta yi bikin cika shekaru 10 da fitar da jigo akan harsuna na taron KAPFEST na Uku

Ƙungiyar Poetic Wednesdays ta gudanar taron Eid Pop-Up a ranar Asabar, 6 ga Yuni, 2026, domin bikin cika shekaru goma da kafuwarta tare da bayyana sabon jigon bikin Kano International Poetry Festival (KAPFEST) karo na uku, mai taken “Reclaiming Languages”, wato ɗabbaka yaruka. An gudanar da taron ne a Alliance Française da ke Kano, inda ya haɗa mawaƙan baka, marubuta, masu sha’awar adabi da sauran jama’a domin tattaunawa, nazari da kuma nishaɗantarwa ta hanyar fasaha. Taron ya kasance wata dama ta waiwayen nasarorin da ƙungiyar ta samu cikin shekaru goma da kuma bayyana shirye-shiryenta na gaba. A yayin taron, an…
Read More
‘Yan sanda sun kama ‘yan ta’addan Lakurawa, Mamudawa da Boko Haram a Kebbi

‘Yan sanda sun kama ‘yan ta’addan Lakurawa, Mamudawa da Boko Haram a Kebbi

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi Rundunar 'yan sanda ta Jihar Kebbi ta samu nasara wurin yaƙi da ta'addanci da garkuwa da jama'a da mallakan makamai ba'a kan ƙa'ida ba.Da yake ma manema labarai bayani a hedkwatar rundunar dake Birnin Kebbi ranar Laraba, Kwamishinan 'yan sanda na Jihar, Umar Hadejia, ya fayyace cewar 'yan ta'addan Lakurawa da Mamudawa da Boko Haram 12, da kuma wanda aka kama da laifin fyaɗe suna nan kulle wurin 'yan sanda, ana share fagen gurfanar dasu gaban kotu. "A ranar 5 ga Yuni 2026, 'yan sandan mobile da ke ofishin 'yan sanda na Illo,…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta samar da fitulu masu amfani da hasken rana a faɗin jihar

Gwamnatin Katsina za ta samar da fitulu masu amfani da hasken rana a faɗin jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Majalisar zartarwa ta amince da samar da fitulu masu amfani da hasken rana guda talatin talatin da ke gundumomi 361 domin rabawa a makaratun Allo da ke faɗin jihar. A zaman ta karo na tara ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar malam Dikko Raɗɗa majalisar ta kuma amince da matakai na inganta rayuwar al'umma. Muhimman abubuwan da majalisar ta amince da su kamar yadda kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya shaidawa manema labarai a Katsina sauran sun haɗa da samar da rumfunar kasuwanci na zamani guda 2000 a ƙarƙashin shirin haɓaka ƙananan masana'antu da ke…
Read More
Me ya sa littattafan Hausa suka gaza gogayya da sauran littattafai na harsunan duniya?

Me ya sa littattafan Hausa suka gaza gogayya da sauran littattafai na harsunan duniya?

Daga ZAHARADDEN IBRAHIM KALLAH Bayan wani gajeren rubutu da na yi a kan gasar gajerun labarai ta Bashir Othman Tofa da aka gudanar a Kano, na samu tambayoyi a kan yanayin da littattafan Hausa suke ciki, musamman na rashin ingantattun zarurrukan labarai da kyan bugu littattafai da rashin kyakkyawan tsarin kasuwancin su a Najeriya ta yadda za a yaɗa su a duniya? Akwai waɗanda suke ganin su kansu marubutan ba su samu gudunmawar da ta dace ba, inda sabbin marubuta ma ba sa samun kulawa da gata na horon da ya kamata, kamar yadda takwarorinsu na Turanci suke samu. Tabbas…
Read More
Sharhin littafin ‘Duhun Damina’

Sharhin littafin ‘Duhun Damina’

Daga BAMAI ALHAJI DABUWA Sunan Marubuciya: Maryam Abdul. Shekarar Bugu: Babu. ISBN: 978-978-982-968-4. Mai Sharhi: Bamai Dabuwa. Lambar Waya: 07037852514. Gabatarwa/Abubuwan Burgewa: Littafin 'Duhun Damina' littafi ne da aka yi amfani da wani irin salo mai kama da tafiyar kura. Shi ne littafin da ya kawo zunzurutun kuɗi sama da miliyan guda a ranar da aka ƙaddamar da shi. Littafin ya taɓo wata matsala da kusan kowa ke tsoron taɓawa saboda gudun tambayar kai ta ya aka yi ka sani? Wasu kuma hankalinsu bai kai wajen ba, musamman iyaye, amma kuma rayuwar 'ya'yansu ce dumu-dumu a ciki. Littafi ne da…
Read More
‘Yan sanda sun kama budurwa da zargin halaka kakarta ‘yar shekara 97 a Katsina

‘Yan sanda sun kama budurwa da zargin halaka kakarta ‘yar shekara 97 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina 'Yan sanda sun kama wata budurwa Aisha Muktar Hassan yar shekara 20 da haihuwa bisa zargin halaka kakarta Hajiya ummukhutsum Hassan mai shekara 97 a garin Daura. Kamar yadda jami'in yaɗa labarai na rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar,mahaifin yarinyar Muktar Hassan ya Kai rahoton kisan kan ga ofishin yan sanda da ke Sabon Garin Daura. DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa saɓani ya shiga tsakanin su inda nan take Aisha Muktar ta ɗauki kujerar katako da buga ma tsohuwar a kai. Ya ce bayan samun rahoton lamarin nan da…
Read More
NBA ta karrama Alƙali Pindiga

NBA ta karrama Alƙali Pindiga

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), reshen Jihar Gombe, ta karrama tsohon babban alƙalin alƙalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga da lambar yabo ta ƙwarewa saboda gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin shari’a da tabbatar da adalci. An gabatar da lambar yabon ne a wani taro da ya samu halartar lauyoyi, alƙalai, jami’an gwamnati da sauran manyan baƙi a Gombe. Shugaban NBA na reshen Gombe, Alhassan Mu’azu, ya ce an yi wa Mai Shari’a Pindiga wannan karramawa ne saboda jajircewarsa, gaskiyarsa da kuma irin rawar da ya taka wajen ƙarfafa tsarin shari’a a jihar.…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su riƙa bayar da rahotannin tsaro cikin kula da haƙƙin kowanne ɓangare

Gwamna Raɗɗa ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su riƙa bayar da rahotannin tsaro cikin kula da haƙƙin kowanne ɓangare

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira ga masu kafafen sada zumunta, masu rubutun yanar gizo (bloggers), da masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet da su kasance masu kula da haƙƙi wajen bayar da rahotannin da suka shafi tsaro, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tallafa wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar. Da yake zantawa da manema labarai bayan wasu jerin ganawa da ya yi a gidan gwamnatin Jihar Katsina tare da malamai da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnan…
Read More