17
Jun
Daga UMAR GARBA a Katsina Babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin ta’addanci. Kotun ta samu matar da laifin safarar harsasai 438 zuwa wani shugaban ‘yan bindiga da ke maɓoyarsa a dajin Dunburum. Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifuffukan da suka shafi ta’addanci. Mai shari’a A.B. Bawale ne ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da cewa an same ta da laifin haɗa baki da kuma taimaka wa ayyukan ‘yan ta’adda. Kotun ta ce…
