16
Jun
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta kara zuba jari a ci gaban Ilimin ƙananan yara na farko, ECD, tana mai cewa koyon wasa yana da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa nishadi da ƙwarewa ga yara ƙanana da kuma bunƙasa ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci. Hukumar ta yi wannan kiran ne a ranar Litinin ta hannun mai taimakawa UNICEF na ƙasa a fannin ECD, Dr. Adamu Gaya, yayin ayyukan bikin Ranar Wasan Yara ta duniya a makarantar Smart School da ke Gusau. An…
