16
Jun
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Daga satar shanu da hare-haren karkara, matsalar ’yan bindiga a Nijeriya ta rikiɗe zuwa wata babbar masana’antar aikata laifuka da ta haɗa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, kai hare-hare kan ƙauyuka, karɓar haraji daga al'umma da kuma tilasta wa dubban mutane barin muhallansu. A yankunan Arewa maso Yamma, dazuzzukan da suka mamaye jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da wasu sassan Kaduna sun zama mafaka ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke kai hare-hare kan matafiya da ƙauyuka kafin su koma cikin dazuzzukan. Rahoton cibiyar bincike ta SBM Intelligence ya nuna cewa tsakanin…
