01
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sanar da shirin gudanar da wani gagarumin bikin aurar da zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wanda ya haɗa da maza 1,500 da mata 1,500. Sheikh Aminu Daurawa, shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano ne ya bayyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba. Shirin, wanda aka sanya wa suna “Auran Gata”, an ce ya fi mayar da hankali ne kan marayu da kuma ’ya’yan talakawa domin tallafa musu su samu ingantacciyar rayuwa ta hanyar aure.…
