01
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An fara sauraron shari’ar da ake yi cikin gaggawa kan wasu mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulki a kan gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda wata muhimmiyar shaida daga rundunar soji ta bayyana wa kotu cewa an raba sama da Naira miliyan 600 domin aiwatar da shirin, tare da alaƙanta tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, da wasu bayanan kuɗi da aka gano a bincike. Shaidar, wani jami’i daga rundunar ’yan sandan sojin Nijeriya, wato Nigerian Army Corps of Military Police (NACMP), wanda aka ɓoye sunansa da laƙabin “AAA”, ya bayyana a…
