ukarofi

12568 Posts
Karamar Hukumar Taura ta kashe miliyan N68 wajen gyaran asibiti — Zarga

Karamar Hukumar Taura ta kashe miliyan N68 wajen gyaran asibiti — Zarga

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Taura da ke jihar Jigawa, Dakta Shu'aibu Hambali Zarga, ya bayyana cewa ƙaramar hukumar ta kashe kimanin Naira miliyan 68 wajen gyarawa da sabunta asibitin Taura, a wani yunƙuri na inganta harkokin kiwon lafiya a yankin. Zarga ya ce wannan mataki na daga cikin manufofin ƙaramar hukumar na tabbatar da cewa al’ummar yankin suna samun ingantattun ayyukan jinya cikin sauƙi. Ya ƙara da cewa a halin yanzu asibitin na da likitoci uku da ke kula da marasa lafiya a kullum. Shugaban ƙaramar Hukumar ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema…
Read More
Kwalejin Shari’ah ta Aminu Kano ta cika shekara 50 — Jakada

Kwalejin Shari’ah ta Aminu Kano ta cika shekara 50 — Jakada

Daga SULAIMAN HUSSAINI, D/Kudu Kwalejin Addinin Musulunci da Shari’ah ta Aminu Kano (Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies) ta cika shekara 50 da kafuwa, inda aka samu gagarumar nasara da ci gaba musamman a fannin shari’ah a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya. Shugaban kwalejin, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai bayan ƙaddamar da shirin bikin cikar kwalejin shekaru 50, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Abdullahi Umar Ganduje da ke harabar makarantar. Jakada ya ce kwalejin ta yaye manyan alkalai, lauyoyi, limaman Juma’a da ma’aikatan kotuna waɗanda ƙasar…
Read More
Naɗin Murtala Garo: An ajiye ƙwarya a gurbinta — Hon. Kabiru Lalo

Naɗin Murtala Garo: An ajiye ƙwarya a gurbinta — Hon. Kabiru Lalo

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU An bayyana naɗin Hon. Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano a matsayin wanda ya dace, tare da cewa an “ajiye ƙwarya a gurbinta”. Hakan ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin kodinetocin mataimakin gwamnan a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Hon. Kabiru Ali Lalo, yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce al’ummar jihar da dama sun nuna farin ciki da wannan naɗi, duba da yadda Garo ke da farin jini musamman a wajen matasa. A cewarsa, hakan zai taimaka wajen bunƙasa siyasa da ci gaban jihar Kano. Ya ƙara da cewa…
Read More
Ba wani gwamna da ya yi wa Kano aiki kamar Abba — Auwalu Soja

Ba wani gwamna da ya yi wa Kano aiki kamar Abba — Auwalu Soja

Daga SULAIMAN HUSSAINI, D/Kudu Kakakin jam’iyyar APC a jihar Kano, Kwamaret Auwalu Soja Sani Mai Nagge, ya bayyana cewa jihar Kano ba ta taɓa samun gwamnan da ya yi mata aiki kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba. Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce ko tsofaffin gwamnoni da ake yabawa ba su kai irin ayyukan da gwamnan na yanzu ya yi cikin ƙanƙanin lokaci ba. Ya ce daga cikin ayyukan da aka gudanar akwai inganta hanyoyi, gyaran makarantu da asibitoci, samar da kayan aiki na zamani, tallafawa matasa da mata da jari,…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mai shago, sun ƙone kadarori a wani ƙauye a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mai shago, sun ƙone kadarori a wani ƙauye a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum mai shekaru 60 tare da ƙona wasu kadarori a yayin wani hari da suka kai ƙauyen Gidan Wando da ke ƙaramar H toukumar Bakori a jihar Katsina. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:06 na yammacin ranar Talata, lokacin da maharan, waɗanda suka zo kan babura kimanin guda 17, suka mamaye ƙauyen tare da buɗe wuta kan al’umma. Rahotanni sun nuna cewa haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da kuma ‘yan sa-kai sun gaggauta kai ɗauki, inda suka…
Read More
Gwamnan Kaduna ya yi umarnin hanzarta kammala titin Nnamdi Azikiwe don daƙile haɗurra

Gwamnan Kaduna ya yi umarnin hanzarta kammala titin Nnamdi Azikiwe don daƙile haɗurra

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da umarni da a gaggauta kammala aikin titin Nnamdi Azikiwe, domin daƙile yawaitar haɗurra da ke haddasa asarar rayuka. Umarnin ya biyo bayan wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki suka gudanar bisa umarnin Gwamna Uba Sani, wanda ya nuna matuƙar damuwarsa kan karuwar haɗɗura a kan titin mai tsawon kilomita 21.5. Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana damuwar gwamnan tare da jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa. Ya ce, “Gwamna ya nuna matuƙar damuwa kan asarar rayukan da…
Read More
Tinubu ya amince da tallafin Naira biliyan biyu ga waɗanda harin Filato ya shafa

Tinubu ya amince da tallafin Naira biliyan biyu ga waɗanda harin Filato ya shafa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da bayar da Naira biliyan 2 a matsayin tallafin agaji ga waɗanda harin da aka kai a ranar 29 ga Maris a Angwan Rukuba, Jos, ya shafa, yayin da ya buƙaci shugabanni da masu ruwa da tsaki su rungumi zaman lafiya domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke yawan faruwa a jihar Filato. Ministan harkokin jinƙai, Mohammed Dorro, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani zama na tattaunawa da aka gudanar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i uku. Taron ya…
Read More
Sojoji sun yi nasarar halaka ’yan ta’adda 11 a Yobe

Sojoji sun yi nasarar halaka ’yan ta’adda 11 a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dakarun rundunar tsaro ta Operation Haɗin Kai sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 11 a wani samame na musamman a iyakar Jihar Yobe. Kakakin rundunar ta musamman, Laftanar- Kanar Sani Uba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wannan Larabar. Ya bayyana cewa sun hallaka ‘yan ta’adda ne bayan samame da suka kai maɓoyarsu da ke Mar, Subdu, Yaro Lawanti da Yaro Shuwari da sauran wuraren da ke kewaye da dajin Bulabulin. Uba ya ce jami’an tsaron sama sun taimaka ƙwarai wajen bayar da bayanan sirri da sanya ido da kuma shirya yadda…
Read More
An nemi hukumomi su shawo kan tashin farashin fetur da siminti

An nemi hukumomi su shawo kan tashin farashin fetur da siminti

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano Wani ɗan kishin ƙasa kuma mai fafutukar ci gaban al’umma, Dakta Jibril Gambo Hadejia, ya bayyana damuwarsa kan rikice-rikicen da ke faruwa a wasu ƙasashen da Nijeriya ke mu’amala da su, musamman a fannin samar da muhimman kayayyaki kamar man fetur da siminti. Ya ce waɗannan rikice-rikice na da tasiri kai tsaye wajen hauhawar farashin kayayyakin, duk da cewa Nijeriya na da yalwar rijiyoyin man fetur da kuma masana’antun siminti. Dakta Gambo ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin man fetur da na siminti da su ɗauki matakan da za su rage tsadar…
Read More
2027: ADC ta rubuta wasiƙa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya don gaggauta hukunci kan rigimar shugabancin jam’iyyar

2027: ADC ta rubuta wasiƙa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya don gaggauta hukunci kan rigimar shugabancin jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban INEC Amupitan na kitsa maƙarkashiyar murkushe duka jam’iyyun banda APC kadai, muna kira da a tsige shi – ADC Jam’iyyar ADC ta rubuta saƙo zuwa ga alƙalin alƙalai ta Nijeriya, Kudirat Kekere-Ekun, inda ta buƙaci da ta sa baki wajen gaggauta yanke hukunci kan rikicin shugabanci da jam’iyyar da ke gaban kotun ƙoli. A cikin wasiƙar da aka aike wa da ofishin alƙalin alƙalan a ranar Talata, lauyan ADC, S. E. Aruwa (SAN), ya ce, ci gaba da jan ƙafa da aka samu ka iya jefa jam’iyyar cikin halin rasa damar shiga a…
Read More