01
May
Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Wani gagarumin goyon baya na ƙara ƙarfi ga Zakariya Jidda yayin da mambobin ƙungiyar APC Youth Solidarity Group a Jihar Gombe suka fito fili suna marawa yiwuwar tsayawarsa takarar kujerar Majalisar Wakilai baya gabanin zaɓen 2027. Wannan goyon baya na zuwa ne bayan shirin Jidda ma daukar nauyin tura matasa 30 daga ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye zuwa ƙasar China domin karatu, wani mataki da ake kallonsa a matsayin zuba jari mai muhimmanci wajen bunƙasa ilimin matasa da inganta rayuwarsu. A wani taron tattaunawa da aka gudanar a Funakaye, hedikwatar ƙaramar hukumar Bajoga, ƙungiyar…
