02
May
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Kwalejin Nazarin Shari’a da Addinin Musulunci ta Aminu Kano (ACSILS) na ƙasa, Alhaji Mahmud Garba Kabuga, ya bayyana matuƙar jin daɗi da farin ciki bisa cikar makarantar shekaru 50 da kafata. Ya ce babu abin da za su ce dangane da wannan gagarumin ci gaba face godiya ga Allah, duba da yadda manufofi da dalilan da aka kafa makarantar a kai suka cika. A cewarsa, hangen nesan magabata ya tabbata, domin makarantar ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa harkar shari’a. Kabuga ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da…
