02
May
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Hukumar majalisar bada shawara kan jam'iyyun siyasa, IPAC, ta zaɓi sabbin shugabannin ta a Jihar Zamfara, ba tare da hamayya ba don gudanar da harkokin hukumar na tsawon shekaru biyu masu zuwa. An gudanar da zaɓen a jiya Juma'a, a hedikwatar hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta, INEC, da ke Gusau, wanda wakilan hukumar IPAC na ƙasa suka jagoranta, kuma jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, da hukumomin tsaro suka shaida. Waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Sulaiman Salisu na Jam'iyyar Action Peoples' Party, APP, a matsayin Shugaba, Bashir Abdullahi Bungudu…
