03
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas ta hana shugabannin kamfanin Shoprite sayar da duk wani kadara ko hannun jari na kamfanin har sai an biya bashin hukunci da ya kai Naira biliyan 1.76 gaba ɗaya. Alƙalin kotun, Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa, ne ya bayar da wannan umarni bayan wata buƙata ta gaggawa da aka shigar a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, domin tabbatar da aiwatar da hukuncin sulhu da kotu ta riga ta amince da shi tun ranar 22 ga Yuli, 2025. Baya ga hana sayar da kadarori, kotun ta kuma umurci shugabannin…
