ukarofi

12568 Posts
Na fito takara ne don ci gaban Ungogo da Minjibir – Zaharaddeen Haruna

Na fito takara ne don ci gaban Ungogo da Minjibir – Zaharaddeen Haruna

Daga Ibrahim  Muhammad  Kano. Wani ɗan siyasa daga yankin Ungogo yace ya  fito neman takara ne don taimakawa al'ummar yankinsa na Ungogo da Minjibir a majalisar tarayya a ƙarƙashin ADC. Dan takara Hon. Zaharaddin Haruna ya ce idan Allah ya sa ya yi  nasara a zaɓen 2027 zai baiwa harkar ilimi da lafiya muhimnanci da kula da matasa  maza da mata da sauran fannoni  don samun cigaba. Matsayin da yake nema al'ummar karamar hukumar ne suka buƙaci ya fito ba zaɓin kansa  bane, idan Allah ya bashi nasara ba zai ba su kunya ba. Ya nuna farin cikin sa da…
Read More
Na shiga harkokin siyasa ne don taimakon al’umma, inji Adamu Danchina

Na shiga harkokin siyasa ne don taimakon al’umma, inji Adamu Danchina

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi Shahararren ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa a fannin ma’adinai a jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya, Alhaji Abdullahi Adamu Danchina, ya bayyana kudirinsa na ci gaba da shiga harkokin siyasar Nijeriya domin taimaka wa al’umma su samu abin yi, ingantacciyar rayuwa da kuma tsaro. Danchina ya bayyana hakan ne a garin Narabi yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce halin da Nijeriya, musamman yankin Arewa, ke ciki a halin yanzu abin tausayi ne. Ya ce a kullum yana shiga daji domin aikin haƙo ma’adinai, inda ake yawan kiransa ba ƙaƙƙautawa don…
Read More
Shugabannin kasuwannin kayan gwari a Kaduna sun koka da ɓullar tsutsar sharon

Shugabannin kasuwannin kayan gwari a Kaduna sun koka da ɓullar tsutsar sharon

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugabannin kasuwannin kayan gwari a Jihar Kaduna sun bayyana damuwa kan yadda wata sabuwar tsutsa da ake kira “Sharon” ke ci gaba da lalata amfanin gonaki, lamarin da ke jefa manoma cikin asara mai tsanani. Rahotanni sun nuna cewa matsalolin da ke addabar manoman kayan miya ba sabon abu ba ne, sai dai zuwan wannan tsutsa ya ƙara dagula al’amura fiye da yadda aka saba gani a baya.  Shugabannin kasuwannin da ke yankunan ƙananan Hukumomin Kubau da Soba sun bayyana cewa duk da ƙoƙarin da ake yi na magance kwari, wannan tsutsa ta fi ƙarfin…
Read More
MURIC ta buƙaci a yi adalci a shari’ar zargin cin zarafin ƙaramar yarinya a Ogun

MURIC ta buƙaci a yi adalci a shari’ar zargin cin zarafin ƙaramar yarinya a Ogun

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ƙungiyar kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) reshen Jihar Ogun ta yi kira mai ƙarfi ga hukumomi da su tabbatar an yi adalci kan zargin cin zarafin wata yarinya mai shekaru 11 a garin Mowe, tana mai gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na rufe shari’ar ba zai samu karɓuwa ba. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Afrilu, 2026, lokacin da yarinyar ke dawowa daga makarantar Islamiyya a kan titin Peace Lane, inda ake zargin wani mutum mai suna Michael ya tare ta tare da kai ta wani gini da ba a kammala…
Read More
Tsaro ya inganta a Fambeguwa, inji Babban Sarkin Kasuwa

Tsaro ya inganta a Fambeguwa, inji Babban Sarkin Kasuwa

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin Kasuwar Fambeguwa a ƙaramar hukumar Fambeguwa da ke jihar Kaduna, Alhaji Nura Usman Oska, ya bayyana cewa a halin yanzu yankin na samun ingantaccen tsaro, inda ya ce ba su da matsalar ’yan ta’adda ko masu aikata laifuka kamar yadda ake samu a wasu wurare. Ya bayyana hakan ne a ofishinsa da ke Fambeguwa yayin da yake zantawa da manema labarai kan halin tsaro a yankin. A cewarsa, an samu gagarumin ci gaba a bangaren tsaro sakamakon ƙoƙarin jami’an tsaro na gwamnati da na sa-kai, waɗanda ke bakin ƙoƙarinsu wajen kare rayuka da dukiyoyin…
Read More
Zargin cin amanar auren Sahabi da Farida Matawalle ya janyo tsegumi a soshiyal midiya

Zargin cin amanar auren Sahabi da Farida Matawalle ya janyo tsegumi a soshiyal midiya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kafofin sada zumunta sun cika da tsegumi da muhawara bayan zargin cewa, Sahabi Liman, mijin Faridah Bello Matawalle, ya shiga wata badaƙalar cin amana makonni kaɗan bayan ɗaurin aurensu mai armashi. Faridah ita ce ɗiyar Bello Matawalle, ƙaramin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara. An gudanar da aurenta da Sahabi ne ranar 6 ga Fabrairu, 2026, a Babban Masallacin ƙasa da ke a Abuja, cikin wani gagaruimin bikin aure da ya ja hankalin jama’a. Rahotanni da ke yawo sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan wata mata mai suna Maryam ta wallafa wasu…
Read More
Surikin Dangote ya bada shawarar soke ranakun hutu a Nijeriya

Surikin Dangote ya bada shawarar soke ranakun hutu a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jamil Abubakar, surukin attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote, ya tayar da muhawara a kafafen sada zumunta bayan ya ba da shawarar cewa ya kamata a soke dukkan ranakun hutu a Nijeriya domin ƙara yawan aiki da bunƙasa tattalin arziki. A wani saƙo da ya wallafa, Jamil ya bayyana cewa Nijeriya na baya sosai idan aka kwatanta da sauran ƙasashe, don haka akwai buƙatar ƙara ƙaimi domin cike giɓin da ke akwai. Ya ce idan aka rage ko aka soke hutun gwamnati da na ƙarshen mako, hakan zai bai wa jama’a damar mai da hankali sosai kan…
Read More
Kotu ta umarci kamfanonin sadarwa su ci gaba da bada rancen katin waya

Kotu ta umarci kamfanonin sadarwa su ci gaba da bada rancen katin waya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Dubban ’yan Nijeriya masu amfani da layukan sadarwa na iya samun sauƙi nan ba da jimawa ba, bayan da Kotun Tarayya ta yanke hukunci guda biyu da suka rusa hujjar doka da ta sa aka dakatar da ba da rancen kati da data a watan Afrilu. Waɗannan ayyukan rance, ciki har da ɗtraTime na MTN da kuma shirye-shiryen aron data na Airtel, an dakatar da su ne sakamakon sabbin ƙa’idojin lamunin dijital da Hukumar Kula Gasa daKare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta Nijeriya (FCCPC) ta kafa. Dakatarwar ta jefa miliyoyin masu amfani da layuka cikin…
Read More
Cece-kuce ya ɓarke bayan wata ta zargi MTN da hannu a cire kuɗi daga asusun bankin mahaifiyarta

Cece-kuce ya ɓarke bayan wata ta zargi MTN da hannu a cire kuɗi daga asusun bankin mahaifiyarta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ’yar Nijeriya ta janyo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta bayan ta zargi kamfanin sadarwa na MTN da hannu a wani zargin cire kuɗi ba tare da izini ba daga asusun bankin mahaifiyarta. Matar, wadda aka bayyana da sunan @ButterBibi a dandalin ɗ (tsohon Twitter), ta yi iƙirarin cewa an cire sama da Naira 70,000 daga asusun mahaifiyarta a yanayi da ba a bayyana ba. A cewarta, bayan faruwar lamarin, mahaifiyarta ta je banki domin kai ƙorafi, inda aka sanar da ita cewa tsohuwar lambar wayarta ta MTN an sake ba wa wani mutum, wanda ake…
Read More
Rashin bin umarnin kotu ya janyo wa 9Mobile tarar miliyoyin Naira

Rashin bin umarnin kotu ya janyo wa 9Mobile tarar miliyoyin Naira

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun ƙoli ta Nijeriya ta yi watsi da ƙarar da kamfanin sadarwa na 9Mobile (wanda ke aiki a ƙarƙashin sunan Emerging Markets Telecommunications Services Ltd) ya shigar, inda ta tabbatar da hukuncin biyan dala miliyan 43.3 da aka yanke masa a shari’ar sasanci, tare da zora masa tarar Naira miliyan 20 kan abin da ta kira “ƙarar da ba ta da tushe”. Hukuncin ya fito ne daga kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Tyjani Abubakar, wanda ya tabbatar da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da kuma Babbar Kotun Tarayya da suka bai wa kamfanonin AFDIN Ventures…
Read More