03
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga, Rabon Albarkatu da Harkokin Kuɗi (RMAFC) ta fara wani muhimmin shiri na tantance bayanai a dukkan jihohin Nijeriya da Babban Birnin Tarayya Abuja, domin inganta tsarin rabon kuɗaɗen shiga na ƙasa da tabbatar da adalci wajen rabon albarkatu. Shirin, wanda ake gudanarwa a faɗin ƙasar baki ɗaya, na da nufin sake duba muhimman ƙa’idoji da ƙididdiga da ake amfani da su wajen raba kuɗaɗen shiga tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi, tare da daidaita su da halin tattalin arziki da zamantakewa na yanzu. Shugaban hukumar, Mohammed Bello Shehu, ya bayyana wannan mataki a…
