ukarofi

12568 Posts
Sanata Yar’adua ya raba tallafin kayan sana’o’i da kuɗin su ya kai Naira biliyan 1.58 a Katsina

Sanata Yar’adua ya raba tallafin kayan sana’o’i da kuɗin su ya kai Naira biliyan 1.58 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da wani tallafi na sana’o’i da kayan more rayuwa da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 1.58, wanda Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua mai wakiltar Katsina ta Tsakiya ya samar domin inganta rayuwar al’umma. An gudanar da ƙaddamarwar a filin wasa na Muhammadu Dikko dake cikin birnin katsina ,inda aka raba kayayyaki iri-iri da za su taimaka wajen ƙarfafa sana’o’i da rage zaman kashe wando a tsakanin jama’a. Daga cikin kayayyakin da aka rabawa al’umma akwai motoci 40 da aka miƙa ma shugabannin jam’iyya, ƙungiyoyin addinai da…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga ɗauke da muggan makamai a kan bubura sun kai hare hare a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Kankiya ta jihar Katsina. Sai dai jami'an tsaro ƙarƙashin DPO na Kankia sun kai wa al'ummar wuraren ɗauki bayan da suka sami bayanan sirri na yadda 'yan bindigan suka mamaye ƙauyukan. Bayan ɗauki ba daɗi na tsawon lokaci da jami'an tsaron, yan bindigan suka gudu suna ɗauke da raunuka da dama. Kwamishinan cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu'azu Danmusa wanda ya sanar da cewa ya ce jami'an tsaron sun sami nasarar kama babura da…
Read More
Obi da Kwankwaso sun kai ziyara hedikwatar NDC a Abuja

Obi da Kwankwaso sun kai ziyara hedikwatar NDC a Abuja

Daga USMAN KAROFI Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun kai ziyara hedikwatar jam’iyyar Nigerian Democratic Congress (NDC) da ke Abuja a ranar Lahadi. Haka kuma, Sanata Victor Umeh ya halarci taron, abin da ya ƙara jawo hasashen cewa suna shirin shiga jam’iyyar. Rahotanni sun nuna cewa wannan ziyara ta zo ne bayan Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ya danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa a shugabanci. A ‘yan watannin nan, ana alakanta shi da yunƙurin kafa wata babbar haɗakar jam’iyyun adawa…
Read More
Al’ummar Wase sun nemi Ahmed Idris Wase ya sake takarar Majalisar Tarayya a karo na 6

Al’ummar Wase sun nemi Ahmed Idris Wase ya sake takarar Majalisar Tarayya a karo na 6

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, Jos Al'ummar mazaɓar kujerar ɗan Majalisar Tarayya ta Wase a Jihar Filato da magoya bayan Jam'iyyar APC ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Wase Equity Projects, sun haɗa kuɗi har Naira Miliyan 10 domin saya wa tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, kuma ɗan majalisa mai wakiltar Wase, Ahmed Idris Wase, takardar neman tsayawa takara, domin ya cigaba da wakiltar yankinsu a Majalisar Ƙasa. Dubban jama'a ne maza da mata suka yi cincirindo don tarbar ɗan majalisar da tawagarsa, yayin da ya shiga garin Wase, domin amsa kiran jama'ar mazaɓarsa da suka neme shi saboda su…
Read More
NUJ a Katsina ta jaddada ƙudirinta na ƙarfafa da kare haƙƙin ‘yan jarida a jihar

NUJ a Katsina ta jaddada ƙudirinta na ƙarfafa da kare haƙƙin ‘yan jarida a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar yan jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina ta jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa kare yancin yan jirada wanda ginshiƙi ne na ɗorewar demokradiyya. A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun shugaba da sakataren ƙungiyar a Katsina Aminu Garba Danɗagoro da Abbas Bamalli, ƙungiyar ta nuna damuwa kan yadda a ke cin zarafi da katsalandan ga aikin jarida. Ƙungiyar itama ta bi takwarorinta wajan bikin ranar yancin 'yan jarida ta duniya. Ƙungiyar ta ce wannan matsala ga yancin 'yan jarida kamar yadda tsarin mulkin ƙasa kuma na iya kawo rauni ga dimokuraɗiyya. "Ya…
Read More
An gano haƙorin ɗan Adam da ya shekara miliyan 1.8

An gano haƙorin ɗan Adam da ya shekara miliyan 1.8

Wasu masana Ilimin Kimiyyar Kayan Tarihi sun gano wani hakorin ɗan Adam a Jojiya da ke ƙasar Amurka, da ya kai shekaru miliyan 1.8. Wannan binciken nasu ya tabbatar na mutane farko-farko ne da suka yi rayuwa a nahiyar Turai. An gano hakorin a kusa da kauyen Orozmani mai tazarar kilomita 100 daga Kudu maso Yammacin Tbilisi, babban birnin Jojiya da kuma kusa da Dmanisi. A garin na Dmanisi ne a ƙarshen shekarar 1990 zuwa farkon 2000, aka gano ƙoƙon kawunan mutane waɗanda aka yi hasashen sun kai shekaru miliyon 1.8. a ƙarƙashin ƙasa. Binciken ya gano cewa, mutanen sun…
Read More
An girbe kabewa mai nauyin kilo 1,158.475

An girbe kabewa mai nauyin kilo 1,158.475

Wani mutumin birnin New York da ke ƙasar Amurka ya kafa tarihi bayan da aka auna kabewarsa guda ɗaya aka gano ta fi tan guda. Manomin mai suna Scott Andrusz na garin Williamsbille, ya kai babbar kabewar tasa ce zuwa gonar Great Pumpkin Farm da ke Clarence, New York, inda aka auna ta aka gano ta kai nauyin kilo 1,158.475. Kabewar ta Andrusz ta karya tarihin kabewa mafi girma da aka taɓa samu a ƙasar Amurka mai nauyin kilo 1,146.682 a baya. Sai dai duk da haka kabewar ba ta karya tarihin da aka kafa a Kundin Tarihi na Duniya…
Read More
Ta haifi ’yan biyu a cincirindon karɓar tallafi a Kebbi

Ta haifi ’yan biyu a cincirindon karɓar tallafi a Kebbi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata mace mai suna Mallama ta haifi jarirai maza tagwaye a yayin wani taron tallafa wa mata da aka gudanar a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi. Rahotanni sun nuna cewa taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, tare da mai ɗakinsa Hajiya Zainab Nasare, inda dubban mata suka taru domin samun tallafin kuɗi don bunƙasa sana’o’insu. An shirya taron ne ƙarƙashin wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna “Mu gudu tare, mu tsira tare”, inda aka gudanar da shi a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi. A lokacin da ake…
Read More
Dalibai miliyan 1.38 sun amfana da rancen karatu – NELFUND

Dalibai miliyan 1.38 sun amfana da rancen karatu – NELFUND

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Asusun Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND), ya bayyana cewa aƙalla ɗalibai 1,388,592 sun riga sun amfana da shirin lamunin karatu da gwamnati ta ƙaddamar. Rahoton yau da kullum da asusun ya fitar ranar Litinin ya nuna cewa tun bayan fara shirin, an karɓi jimillar buƙƙatun lamuni 1,778,854 daga ɗalibai a faɗin ƙasar. An kuma samu ƙarin buƙatu guda 353 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata, yayin da kaso na ƙaruwa ya tsaya a matakin kashi 0.0. Dangane da kuɗaɗen da aka fitar, NELFUND ya bayyana cewa zuwa ranar 2 ga Afrilu, 2026, an biya…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata rahoton ƙaddamar da sabon harajin motoci

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata rahoton ƙaddamar da sabon harajin motoci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Karɓar Haraji ta ƙasa (NRS) ta ƙaryata wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon haraji kan motoci daga ranar 1 ga Yuli, 2026, tana mai cewa bayanin ƙarya ne kuma an yi shi ne don yaudarar jama’a. Hukumar ta bayyana cewa hoton da ke yawo ya umarci masu motoci su biya wani haraji ta yanar gizo ko a bankuna, duk da cewa bai bayyana ƙimar harajin ba, kuma ba shi da sahihin tushen inda ya fito ko marubuci. An kuma lura cewa an…
Read More