ukarofi

12568 Posts
Matsalar fanshon ’yan sanda: Buƙatar gaggawar gyara don kare martabar masu ritaya

Matsalar fanshon ’yan sanda: Buƙatar gaggawar gyara don kare martabar masu ritaya

Zuwa ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Masu Ruwa da Tsari, Assalamu alaikum. Wannan wasiƙa na zuwa ne cikin girmamawa da kuma nuna damuwa mai zurfi dangane da halin ƙunci da wahala da tsoffin jami’an ’yan sandan Nijeriya ke fuskanta bayan sun kammala hidimarsu ga ƙasa. Lamarin ya zama abin takaici matuƙa, har ya kai ga haifar da zanga-zanga, koke-koke da kuma kiraye-kirayen neman gyara daga waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare doka da oda a cikin al’umma. Ba sabon abu ba ne cewa batun fansho na ’yan sanda ya daɗe yana jan hankali a ƙasar nan. Tun bayan ƙaddamar…
Read More
Nakasa a mahangar karin magana: Guzurin Ranar Nakasassu ta Duniya 

Nakasa a mahangar karin magana: Guzurin Ranar Nakasassu ta Duniya 

Daga MUJAHEED ABDULLAHI KUDAN Shimfiɗa tabarma: Nakasa na nufin tawaya ko gaza ko raunana, (CNHN, 2006: 356). Saboda haka, nazarin nakasa fage ne da ke ƙoƙarin bayyana batutuwan da suke ɗamfare da zamantakewa da al’adu da siyasa waɗanda suka jiɓanci yadda ake kallon nakasa da nakasassu. Ita kuwa karin magana ɗaya ne daga cikin sassan adabin baka da Hausawa ke amfani da ita domin ƙawata zance ya yi armashi. Ke nan, karin magana zance ne a dunƙule mai faffaɗar ma’ana, ƙunshe da sharhi kan rayuwar al`umma cikin hikima da fasaha. Shi ya sa karin magana ya zama rumbun ajiye al`adu…
Read More
Gawar Gloria da Linus!

Gawar Gloria da Linus!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Jinjina ga da jami’an tsaro da su ka yi kukan kura zuwa muguwar tungar ’yan ta’addan IP0B a jihar Imo inda hakan ya kai ga gano kabarin da a ke kyautata zaton nan ne a ka binne sojojin nan biyu Warrant Office Linus Audu da Private Gloria Mathew wadanda mugayen irin su ka kashe a shekara ta 2022 lokacin da su ke kan hanyar zuwa ɗaura musu aure a al’adance. A lokacin kisan, mugayen ’yan IP0B da ’yan bindiga daɗinsu ESN sun kashe sojojin da yin gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu, kuma har da naɗar ta’addancin a…
Read More
CBN ya fito da sabbin ƙa’idojin cajin kuɗi da rance ga bankuna

CBN ya fito da sabbin ƙa’idojin cajin kuɗi da rance ga bankuna

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar da sabon daftarin ƙa’idoji da ke nufin rage kuɗaɗen da bankuna ke caji da kuma ƙara sahihanci da gaskiya a tsarin bayar da rance, a wani mataki da ake kallon zai sauƙaƙa wa ’yan ƙasa da ’yan kasuwa harkokin kuɗi. Sabon tsarin, mai taken “Jagorar Kuɗaɗen da Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi ke Caji 2026,” ya zo ne domin sabunta dokokin da aka kafa tun 2020, tare da daidaita su da sabbin sauye-sauyen da ake samu a fannin hada-hadar kuɗi, musamman a ɓangaren biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani. A…
Read More
Kalubalen bazuwar makamai a hannun jama’a 

Kalubalen bazuwar makamai a hannun jama’a 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba mun sha ganin rahotannin da ake bayyanawa a kafafen watsa labarai, dangane da yadda jami'an tsaro ke kama mutane masu safarar ƙananan makamai, da suka haɗa da bindigogi da harsasai. Na san za ka yi mamaki jin cewa daga cikin irin mutanen da ake kamawa har da mata, kuma a cikin su za ka samu akwai Musulmi da Kirista.  Kamar yadda wani mawaƙi a kafar sadarwa ke cewa, 'ɗan iska ba shi da kama!' To, babu shakka haka ne, mugun mutum ba shi da kama, domin kuwa a…
Read More
APC ta tsayar da DCP Mohammed Ahmed a Gombe ta tsakiya, ta ajiye Sanata Goje

APC ta tsayar da DCP Mohammed Ahmed a Gombe ta tsakiya, ta ajiye Sanata Goje

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe A wani gagarumin sauyi da ya girgiza fagen siyasar Jihar Gombe, Jam’iyyar APC ta bayyana tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya, Mohammed Ahmed, a matsayin dan takararta na Sanatan Gombe ta tsakiya gabanin zaɓen 2027, tare da janye tsohon gwamna kuma sanata mai ci, Sanata Danjuma Goje, daga takarar. Wannan mataki ya biyo bayan jerin shawarwari da tuntuɓa da aka gudanar tsakanin manyan shugabannin jam’iyyar, sarakunan gargajiya da wakilan al’umma daga ƙananan hukumomin Yamaltu/Deba da Akko, wadanda ke cikin mazabar Gombe ta tsakiya. Mohammed Ahmed, wanda aka fi sani da “Jarman Deba,” ya samu…
Read More
Kuɗaɗen shiga na Katsina sun ƙaru daga Naira 400m zuwa Naira biliyan uku – Raɗɗa

Kuɗaɗen shiga na Katsina sun ƙaru daga Naira 400m zuwa Naira biliyan uku – Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Raɗɗa yace ci gaban ya samu ne sakamakon tace giɓin shiga da kuma amfani da tsarin TSA. Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sanar da ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) na jihar, wanda ya tashi daga kusan naira miliyan 400 zuwa naira biliyan 3 a kowane wata. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar tawagar kwamishinoni da ma’aikatan hukumar tattara kuɗaɗe, raba su da tsare-tsaren kuɗi ta ƙasa (Revenue Mobilization, Allocation and Fiscal Commission), ƙarƙashin jagorancin Sa’ad Ibrahim Bello, a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a…
Read More
Sarkin Katsina ya taya Sunusi Saulawa murnar zama muƙaddashin provost marshal a hukumar Kwastom

Sarkin Katsina ya taya Sunusi Saulawa murnar zama muƙaddashin provost marshal a hukumar Kwastom

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ta taya Tasi’u Sanusi Saulawa zama muƙaddashin Provost Marshal na hukumar Kwastam ta Najeriya. A wata sanarwa, Sarkin ya bayyana cewa naɗin Saulawa ya zo ne bisa cancanta da ƙwarewa, tare da nuna jin daɗinsa da alfahari ga wannan matsayi da ɗan asalin Jihar Katsina ya samu. Mai Martaba ya ƙara da cewa wannan naɗi babban nauyi ne da ke buƙatar jajircewa, riƙon amana da kuma aiki tuƙuru domin tabbatar da an cika amanar da aka ɗora masa. Sarkin Katsina ya yi addu’ar Allah ya ba Saulawa…
Read More
Lajnatul Hisbah a Katsina ta yi kira ga al’ummar jihar da su mallaki katin zaɓe

Lajnatul Hisbah a Katsina ta yi kira ga al’ummar jihar da su mallaki katin zaɓe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar Lajnatul Hisbah ta ƙasa reshen Jihar Katsina ta buƙaci al’umma musamman waɗanda suka cancanta su kaɗa ƙuri’a, da su gaggauta yin rijistar zaɓe domin mallakar Katin zaɓe na dindindin (PVC) gabanin babban zaɓen shekarar 2027, don zaɓen wakilai nagari. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da ta gudanar a babban ofishinta da ke Masallacin Kandahar, Ƙofar Ƙaura, cikin birnin Katsina. Babban kwamandan ƙungiyar na jihar, Malam Bilyaminu Muhammad Balalarabe, wanda ya jagoranci taron, ya ce lokaci ya yi da jama’a za su fahimci muhimmancin shiga harkokin zaɓe domin tabbatar da…
Read More
Ba a haifar jarumar mace, gina ta ake yi – Marie Curie 

Ba a haifar jarumar mace, gina ta ake yi – Marie Curie 

"ilimi ba kawai hanya ce ta samun aiki ba, hanya ce ta samun ‘yanci" Daga AISHA ASAS  A cikin wannan shafi mai farin jini na Mata A Yau da ke shafukan Gimbiya na Blueprint Manhaja, muna ci gaba da haskaka rayuwar mata jarumai, waɗanda suka tsallake rijiya da baya, suka fuskanci ƙalubalai masu tsanani, amma suka tsaya tsayin daka har suka zama abin koyi ga al’umma. Kamar yadda ku ka sani, wannan shafi ba kawai shafin bayar da labaran rayuwar mata ba ne, wuri ne na ilmantarwa da tunatarwa, inda ake fito da rayuwar mata domin ta zama madubi ga…
Read More