07
May
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan littafi: Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci Mawallafi: Sheikh Abdulƙadir Na'Annabi Mu'azu Shekarar bugawa: 2026 Yawan shafi: 80 Mai sharhi: Abba Abubakar Yakubu Wane ne Sheikh Na'Annabi Mu'azu? Sheikh Abdulƙadir Na'Annabi Mu'azu wani fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ke zaune a Jos, Jihar Filato. Allah Ya yi wa wannan malami baiwar sanin ilimin luggar Larabci da Balagha. Sannan malamin gwani ne wajen rubuta waƙoƙin Larabci da na Hausa, masu ƙunshe da darussa iri-iri. Ya kuma rubuta wasan kwaikwayo na Larabci da suka shafi tarihin Musulunci, da wasu fitattun malaman Musulunci. Sanin Asali…
