ukarofi

12568 Posts
Hare-haren Baƙin Haure: Oshiomhole ya nemi Nijeriya ta kori MTN da DSTv

Hare-haren Baƙin Haure: Oshiomhole ya nemi Nijeriya ta kori MTN da DSTv

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sanatan mai wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Adams Oshiomhole, ya yi kira ga gwamnati da ta soke lasisin kamfanonin Afirka ta Kudu da ke aiki a Nijeriya, ciki har da MTN da MultiChoice, sakamakon sabbin hare-haren ƙiyayyar baƙi da ake kai wa ‘yan Nijeriya a ƙasar Afirka ta Kudu. Kiran nasa ya zo ne yayin da Majalisar Wakilai ta ƙasa ta yi Allah-wadai da sabon tashin hankali, tare da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakan gaggawa na diflomasiyya da kariya domin tabbatar da tsaron ‘yan Nijeriya a ƙasashen waje. Yayin da yake jawabi a…
Read More
Rikicin FCCPC da NCC kan ba da rancen kati na haifar da cikas ga tattalin arziki

Rikicin FCCPC da NCC kan ba da rancen kati na haifar da cikas ga tattalin arziki

Rikicin da ke ci gaba tsakanin Hukumar Kula da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta ƙasa (FCCPC) da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ya jefa kasuwar bashin katin kira da intanet wadda ke da darajar kusan Naira biliyan 400 cikin ruɗani, tare da haddasa cikas ga miliyoyin masu amfani da sadarwa a faɗin ƙsar. Saboda wannan saɓani na doka da iko tsakanin hukumomin biyu, wasu manyan kamfanonin sadarwa sun dakatar da tsarin bayar da rancen katin kira ga abokan hulɗarsu na ɗan lokaci. Wannan mataki ya jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin wahala, musamman masu ƙaramin ƙarfi da suka dogara…
Read More
‘Yan bindiga sun kai hari jami’ar Nasarawa tare da sace ɗalibai shida

‘Yan bindiga sun kai hari jami’ar Nasarawa tare da sace ɗalibai shida

Daga JOHN D WADA a Lafia Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa ta ce ta ƙara ƙaimi wajen ceto ɗalibai shida na Jami’ar Nasarawa da ke Keffi, wadanda ‘yan bindiga suka sace a Gudi, ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar. Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, SP Rahman Nansel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Lafia. SP Nansel ya ce an sace ɗaliban ne a ranar 6 ga Mayu da misalin ƙarfe 9 na dare lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka farmaki wani masauki na…
Read More
2027: Jamilu Gwamna ya sha alwashin haɗa kan Gombe

2027: Jamilu Gwamna ya sha alwashin haɗa kan Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe Dan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, Sardaunan Gombe, ya bayyana ƙudirinsa na gina gwamnati da zai yi tafiya da kowa tare da bunƙasa ci gaba idan aka zaɓe shi a shekarar 2027. Gwamna ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar, inda ya ce babban burinsa shi ne haɗa kan jama’a da tabbatar da ci gaban da zai amfani kowa da kowa. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Sani Shawai, ya fitar, Gwamna…
Read More
Zaɓen 2027: An yi kira ga matasan Katsina su guji bangar siyasa

Zaɓen 2027: An yi kira ga matasan Katsina su guji bangar siyasa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman yayi kira ga matasa a faɗin jihar Katsina musamman yankin Funtua da su guji bangar siyasa domin kyautata rayuwar su da mutuncin su. Kwamred Suleiman yayi wannan kira a Katsina a wata hira da manema labarai inda ya nuna damuwarsa kan yadda matasa suka gujewa karatu da sana'o'i suka koma bin 'yan siyasa. Ya ce wajibi ne matasa su tashi tsaye wajen nema na kansu makamai dubu da halin matsin tattalin arzikin ƙasar. Ya yaba wa gwamna Dikko Raɗɗa kan kafa dokar ta ɓaci kan ƙauraye da bangar…
Read More
Farfesa Abdallah Uba Adamu: Shekaru 70 na ilmi, bincike da sauya tarihi

Farfesa Abdallah Uba Adamu: Shekaru 70 na ilmi, bincike da sauya tarihi

Daga IBRAHIM HAMISU A ranar 25 ga Afrilu, 2026, al’ummar ilimi a Nijeriya, musamman na Jami’ar Bayero da ke Kano, sun yi wa wani babban gwarzon ilimi bankwana na kammala aiki bayan sama da shekaru 40 yana koyarwa, bincike da jagoranci. Ritayar Farfesa Abdallah Uba Adamu ba kawai ƙarshen aikin gwamnati ba ne, a'a wata muhimmiyar alama ce ta cika tafiyar rayuwa mai cike da hidima ga ilimi, al’adu da cigaban al’umma. A tsawon shekarun da ya kwashe yana aiki, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya zama ɗaya daga cikin fitattun malaman jami’a da suka haɗa ilimin kimiyya da na zamantakewa…
Read More
2027: Ƙungiyar Tudun-Gwandara For Wadada sun buɗe ofishin su a hukumance

2027: Ƙungiyar Tudun-Gwandara For Wadada sun buɗe ofishin su a hukumance

Daga JOHN D WADA a Lafia Ƙungiyar yaƙin neman nasarar ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa Sanata Aliyu Ahmed Wadada a Tudun-Gwandara da ake kira Tudun-Gwandara For Wadada Vision 2027 a turance sun gudanar da babban taron buɗe sabon ofishin kamfen na yankin tare da karɓar dinbin magoya bayan 'yan takarar gwamnan da suka janye suka dawo tafiyar Wadada a yankin. A jawabinsa na maraba a wajen taron shugaban tafiyar Wadada a Tudun-Gwandara Comrade Mohammed Maihadishi ya marabci duka waɗanda suka halarci taron dama waɗanda basu samu damar zuwa ba inda yace ƙungiyar Tudun-Gwandara For Wadada Vision 2027 ta shirya…
Read More
‘Yan takarar APC sun ƙi amincewa da masalaha a Katsina

‘Yan takarar APC sun ƙi amincewa da masalaha a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu masu neman takarar kujerun majalisar dokoki a jam’iyyar APC a Jihar Katsina sun sayi fom ɗin takara domin nuna rashin amincewarsu da tsarin sasanci da jam’iyyar ta amince da shi gabanin zaɓen 2027. Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, jam’iyyar APC a jihar ta yanke shawarar fitar da ‘yan takararta ta hanyar maslaha, inda aka kafa kwamitin da tsohon gwamna Aminu Bello Masari ke jagoranta. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilai da sanatoci ba su samu tikitin sulhu ba, lamarin da ya jawo zarge-zargen cewa ana fifita ‘ya’yan manyan mutane…
Read More
Nasarawa 2027: Rikicin magajin Gwamna Sule ya sake ɓarkewa

Nasarawa 2027: Rikicin magajin Gwamna Sule ya sake ɓarkewa

Daga JOHN D WADA Lafia Yayin da rikicin APC na jihar Nasarawa kan wanda za a zaɓa a matsayin ɗan takarar gwamna ya ƙara zurfafa inda tsohon gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya ƙi bayyana a wajen taron zuba jari na gwamnatin jihar da Gwamna Abdullahi Sule ya shirya. Wakilinmu da ya kasance a wajen taron ya gano cewa an shirya taron ne daga 6 zuwa 7 ga Mayu 2026 inda masu zuba jari da aka gayyata suke gabatar da kasidai akan hanyoyin faɗaɗa zuba jari a jihar yayin da mulkin Abdullahi Sule ke gab da kammaluwa. Masu sharhi kan…
Read More
Dambe wasar maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (3)

Dambe wasar maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (3)

Daga IBRAHIM MUHAMMAD  (Danmadamin Birnin Magaji) Waƙoƙin jama'a: Waƙar Sani Kangiwa 1937-2010 (73) Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Sani Adamu ɗanbaba Kangiwa Turakin Kebbi / Argungu Shekarar da aka yi waƙa 1978 Muhallin Waƙa  ƙofar Tsohon Gidan Alhaji Sani Kangiwa da ke Sakkwato Saƙon Mawaƙi/Waƙa Yabo da Kambamawa Waƙar Zubairu ƙofar Rini 1940-1993 (53) Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji Zubairu Tela ɗanmalikin Sakkwato Shekarar da aka yi waƙa 1976 Muhallin Waƙa  ƙofar Gidan Alhaji Zubairu Tela ƙofar Rini Sakkwato Saƙon Mawaƙi/Waƙa ƙauna da Soyayya  Waƙar Aliyu Layi 1934-2002 (68) Sunan wanda aka yi ma waƙa Alhaji…
Read More